Rundunar ‘yansandan Abuja ta sanar da kashe wani shahararren ɗan bindiga mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa Dogo Saleh da yaransa sun addabi wasu sassan birnin Abuja da hare-haren garkuwa da mutane.
- ‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutanen 30 A Katsina
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafawa Duniya Gwiwa Ta Hanyar Fadada Bude Kofar Ta
Ta ce bayan samun bayanan sirri kan maɓoyarsa, jami’an ‘yansanda suka kai samame domin cafke shi.
Sai dai yayin musayar wuta, an kashe shi tare da wasu yaransa.
Dogo Saleh ya kasance babban mataimakin shugabannin ‘yan bindiga da suka yi fice wajen aikata laifuka, musamman a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
SP Adeh ta kuma ce jami’an ‘yansanda sun ceto wasu mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin farmakin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp