‘Yansandan Jihar Kwara sun kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin wata arangama da suka yi a garin Shao da ke karamar hukumar Moro a jihar.
‘Yansandan sun kuma ceto wasu mutane biyu da aka kashe, Afusat Lawal da danta, Taofik Lawal, wadanda masu garkuwa da mutanen suka yi garkuwa da su a ranar Talata.
- Nijeriya Ba Za Ta Bunkasa Ba Sai Da Ingantacciyar Wutar Lantarki – TambuwalÂ
- ‘Yansanda A Ebonyi Sun Damke Wasu Masoya Da Suka Sayar Da Jaririnsu A Kan Kudi N500,000
LEADERSHIP ta tattaro cewa ‘yansanda ne suka gudanar da aikin ceton tare da wasu ‘yan banga da mafarauta a yankin Shao.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, a ranar Laraba ya tabbatar da kashe masu garkuwar tare da ceto mutane biyu.
Ajayi ya ce, “A ranar 13/9/22 da misalin karfe 23:20 na dare an yi garkuwa da wata Afusat Lawal da danta, Taofeek Lawal.
“Rundunar ‘yansandan Jihar Kwara na son sanar da jama’a cewa, an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne bayan wani gagarumin aikin bincike da ceto da ‘yan banga da mafarauta suka yi.
“An kama wasu masu garkuwa da mutane ne a cikin daji a lokacin da suke raba kudin fansa da aka karba daga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda nan take suka bude wuta kan jami’an tsaro, yayin da aka yi musayar wuta da su, an cafke biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen da suka samu raunuka a harbin bindiga a yayin ganawar. Kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), inda aka tabbatar da mutuwarsu.
“Saboda haka, an ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa na asibitin domin a tantance gawarwakinsu.
“Abubuwan da aka kwato daga hannun masu garkuwa da mutanen sun hada da mota kirar Honda Accord Saloon daya dauke da lamba LAGOS GJ 52 LSR da bindiga daya da kuma kudi da ba a tantance adadinsu ba.
Ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an kama wasu da suka gudu domin gurfanar da su gaban kuliya.