Hadin gwiwar jami’an tsaron a jihar a karamar hukumar Alkaleri, sun hallaka ‘yan bindiga uku yayin da sauran suka tsere da raunuka a Jihar Bauchi.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Ahmed Wakili, ya fitar, inda ya ce jami’an rundunar sun samu wannan nasarar ne a ranar jajibirin sabuwar shekarar 2023.
- Mara Wa Dan Siyasa Baya Zubar Da Mutunci Ne – Martanin Kwankwaso Ga Obasanjo
- Albishir Ga ’Yan Kasuwar Ketare Dake Kasar Sin
Ya ce rundunar ta kai wani samame a Dajin Madam da na Yankari.
A cewar sanarwar, jami’an sun ci gaba da yin sintiri a cikin dazukan da nufin cafke sauran da suka tsere.
Har wa yau, ya ce sun kwato bindigu kirar AK-47 biyu.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar ta samu gagarumar nasarar yakar ayyukan ‘yan bindiga a jihar, inda hakan ya hana su sakat, wajen aikata ayyukansu musamman a kauyukan Rimi, Magama Bagwas, Mansur, Pali da Yalo.
An kuma cafke wasu mutune biyu da ake zargin masu satar mutane ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2022.
A cewar sanarwar, wani da ake zargin mai suna Adamu Mohammed mai shekara 33, ya shiga hannu tare da wani mai suna Datti Alhaji Bulama mai shekara 35 wanda aka fi sani da Dattuwa, wadanda mazauna mazabar Maimadi da ke a yankin Pali.
Bincike ya nuna cewa, babban wanda ake zargin Adamu Mumammed, ya amsa laifin da akw tuhumarsa da shi, inda ya ce ya sace mutane hudu a kauyen Kaltanga tare da ajiya su a dajin Yankari har zuwa kwana biyar, har sai da aka biya kudin fansa Naira 20,000,000.