Rundunar ‘yansanda ta jihar Nasarawa ta tabbatar da garkuwa da Sarkin Gurku, Jibrin Mohammed da matarsa da wasu ‘yan bindiga suka yi a garin Gurku da ke karamar hukumar Karu a jihar.
DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan ne ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce an yi garkuwa da sarkin ne a fadarsa.
A cewar Nansel, a ranar 6 ga watan Agusta, rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa ta samu kiran gaggawa cewa wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun mamaye fadar garin Gurku mai tazarar kilomita 10 daga babban garin Mararaba a cikin karamar hukumar Karu.
“Bayan samun labarin, kwamishinan ‘yansandan jihar Nasarawa, CP Maiyaki Mohammed-Baba, ya tura tawagar jami’an ‘yansanda tare da hadin guiwar ’yan banga zuwa wurin.
“Da isowar jami’an, sun iske cewa, tuni an tafi da basaraken da matarsa zuwa wani wurin da ba a san ko ina ba ne.
“An bincike dajin da tsaunukan da ke kewayen garin amma duk kokarin cimmusu ya ci tura,” inji shi.