Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa kawo yanzu babu wani sauran nishadi a harkar kwallon kafa sakamakon rashin bawa ‘yan kallo shiga filin wasa domin kallo.
Guardiola ya bayyana hakan ne duk da nasara mafi girma da kungiyarsa ta Manchester City ta yi a kakar bana, na doke kungiyar Burnley da ci 5-0 a filin wasa na Etihad a ranar Asabar wanda kuma itace nasara ta biyu da yayi a gida tun farkon fara wannan kakar.
Amma duk da haka Guardiola baiyi cikakken gamsuwa da nasarar ba, wato bai nuna alamun murna ba sai dai ya nuna damuwa ne, cewar wasan shine na 29 a jere da Manchester City ke bugawa ba tare da magoya baya ba a cikin filin wasan , kuma hakan lamarin zai kasance a akalla wasanni biyar masu zuwa kafin wata kila a samu sauyin, lokacin da kungiyar za ta je Southampton a ranar 19 ga watan Disamba.
An daina shiga filin wasa tun farko barkewar annobar Korona a kakar wasan data gabata a watan Maris wanda hakan yasa aka dakatar da buga wasanni na tsawon wajen watanni biyar daga baya kuma aka koma wasannin amma ba tare da masu kallo ba