Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa a ƙalla gwamnoni 18 dake mulki a halin yanzu suke ƙarƙashin bincike daga hukumar.
Ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da aka gudanar a Legas a ranar Juma’a. A cewarsa, “Yanzu haka ina gudanar da bincike akan wasu gwamnoni 18 masu ci. Idan suka sauka daga mulki, za mu ɗauki mataki na gaba.”
- EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
- EFCC Ta Kama Ƴan Ƙasashen Waje 146 Kan Laifukan Zambar Kuɗaɗe
Shugaban EFCC ya bayar da labarin yadda wani tsohon gwamna ya tsere zuwa Ingila a rana ta biyu bayan ya mika mulki, saboda yana tsoron a cafke shi. Ya ce tsohon gwamnan ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa a wani otel inda yake liƙin kuɗaɗen ƴan fam fam 50 da fam 10, abin da ya sa manajan Otel ɗin ya kira ‘yansanda (911), yana zargin gwamnan da hauka.
A cewarsa, sai da wasu gwamnoni biyu da sauran abokansa da suka je taron suka shawo kan lamarin a gaban Ƴansandan Burtaniya, suna bayyana cewa tsohon gwamnan ba mahaukaci ba ne, sai dai kawai nuna halin rashin gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp