Connect with us

WASANNI

Yanzu Hankalina Ya Kwanta Tunda Na Fara Cin Kwallo – Ronaldo

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa kawo yanzu hankalinsa ya kwanta tunda ya fara zura kwallo  araga kuma yanzu zai ci gaba da cin kwallaye domin daman aikinsa ne.

Ronaldo dai ya shafe awanni shida bai zura kwallo a raga ba tun  ayan komawarsa kungiyar ta Jubentus abinda ake ganin kamar barin Real Madrid ne ya sa hakan ta kasance kuma baya samun ‘yan wasan da zasu dinga taimaka masa.

Ronaldo ya fara zura kwallo a ragar kungiyar Sassulo wanda hakan yasa magoya bayan Jubentus suka rude da ihu kafin kuma ya sake jefa kwallo ta biyu wadda itace tabawa Jubentus din damar samun maki uku a wasan.

“Rashin zura kwallo a raga har ya fara damuna saboda duk inda Ka duba idan ana maganar Jubentus cewa akeyi har yanzu ban zura kwallo a raga ba hakan yasa na fara tunanin abubuwa da yawa marasa dadi” in ji Ronaldo

Yaci gaba da cewa “kwallon kafa ce daman kuma komai yana ita faruwa a kungiyoyin dana buga a baya ma na taba samun kaina a irin wannan yanayi sai dai surutun bai kai haka ba sai yanzu saboda na bar Real Madrid na koma Jubentus”

Jubentus dai za ta fara buga wasanta na farko na gasar cin kofin zakarun turai a ranar Laraba inda za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Balencia dake kasar sipaniya wasan da ake ganin mai wahala ne ga Jubentus din wadda take da niyyar lashe gasar ta wannan shekarar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: