Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mika mulki domin saukaka tare da tafiyar da shirin mika mulki na shekarar 2023.
Mambobin kwamitin su ne: Sakataren gwamnatin tarayya a matsayin shugaba; Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Antoni-Janar na tarayya da kuma babban sakatare, na ma’aikatar shari’a ta tarayya.
- Buhari Ya Nada Farfesa Magaji, Sabon Shugaban Kwalejin Fasaha Ta Kasa Da Ke Kabo, Jihar Kano
- Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Dan Iya, Ya Musanta Ficewa Daga PDP
Sauran sun hada da Sakatarorin dindindin na ma’aikatun tsaron cikin gida, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa.
Sauran kuma sun hada da; Ofishin Harkokin Majalisa, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Ofishin Janar na Ayyuka, Ofishin Harkokin Tattalin Arziki da Siyasa, Babban Hafsan Tsaro, Sufeto-Janar na ‘yansanda, Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Jiha, Babban Magatakarda na Kotun Koli na Nijeriya; da wakilai guda biyu, wanda zababben shugaban kasa zai nada.
A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na sakataren gwamnatin tarayya ya fitar, zai kaddamar da kwamitin mika mulki a ranar Talata 14 ga watan Fabrairu, 2023.
Har ila yau, shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar zartarwa mai lamba 14 na 2023 game da gudanarwa da sauyin shugaban kasa.
Babban abin da ke cikin dokar zartaswa ta shugaban kasa mai lamba 14 ta 2023 ita ce kafa tsarin shari’a da zai ba da damar mika mulki ba tare da wata matsala ba daga wannan gwamnatin ta shugaban kasa zuwa mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp