Yanzu-yanzu: Buni Ya Sauya Wa Kwamishinoni Biyu Wajen Aiki

Gwamnatin Yobe

Daga Muhammad Maitela Damaturu,

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da kirkiro sabuwar ma’aikatar nemo ingantattun hanyoyin fadada arziki, da nemo ayyukan yi a jihar.

Gwamnatin jihar ta sanar da hakan a takardar manema labaru mai dauke da sa hannun sakataren yada labaru a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Malam Shu’aibu Abdullahi, a Damaturu.

Ya ce bisa kirkiro sabuwar ma’aikatar, Gwamna Buni ya amince da sauya wa kwamishinoni biyu wurin aiki nan take, wadanda su ka hada da Hon. Abdullahi Bego, daga ma’aikatar yada labaru, harkokin yau da kullum da al’adu zuwa sabuwar ma’aikatar, yayin da Hon. Mohammed Lamin, daga ma’aikatar filaye da albarkatun kasa ya maye gurbin sa.

Har wala yau kuma, Gwamna Buni ya amince da mayar da aikace-aikacen ma’aikatar filaye da albarkatun kasa zuwa hukumar kula da bayanan kasa ta Yobe Geographic Information System (YOGIS).

A hannu guda kuma, biyo bayan hakan, ya nuna cewa hukumar bayar da bayanan kasa (YOGIS) ta karbe ayyukan da ma’aikatar filaye da albarkatun kasa a jihar Yobe.

Exit mobile version