Gwamnatin tarayya na ganawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC da TUC game da yajin aikin da suka tsunduma na sai baba-ta-gani a fadin kasar.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Bako Lalong, da karamin ministan ayyuka, Hon. Nkeiruka Onyeajeocha, sun halarci taron da ake gudanarwa a ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).
- Ribadu Ya Bukaci NLC Ta Janye Yajin Aiki, Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Da Aka Yi Wa Ajaero
- Babu Ranar Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira – CBN
Daga bangaren shugabannin kungiyar kwadago, akwai Festus Osifo a karkashin jagorancin shugaban TUC, da babban sakataren kungiyar NLC, Emmanuel Ugboaja, da sauran shugabannin kungiyar kwadagon a wurin taron.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, NLC da TUC sun bayyana tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin Nijeriya domin nuna rashin amincewarsu da kamawa da cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero, da ‘yansanda suka yi a Owerri, jihar Imo a ranar 1 ga Nuwamba, 2023.