Hon. Chiroma Buba Mashio daga mazabar Jajere, ya zama sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, karo na 8.
Hakan ya biyo bayan zaman da majalisar ta kaddamar yau a zauren majalisar dake Damaturu, yayin da aka fara gabatar da kudirin zaben sabon Kakakin Majalisar, wanda Hon. Adamu Dala Dogo mai wakiltar mazabar Karasuwa ya gabatar inda ya samu goyon bayan Hon. Bukar Mustapha na mazabar Geidam ta tsakiya tare da samun amincewar dukkanin yan majalisar dokokin 24.
An haifi Hon. Buba Mashio ranar 25 ga Mayu, a 1968 a garin Mashio a karamar hukumar Fune dake jihar Yobe.
Ya fara karatun sa a firamaren Mashio sannan ya wuce Sakandaren Gwamnati dake Damagum, kuma ya fara aiki a karamar hukumar Fune inda ya yi murabus ya tsaya takarar kansila mai wakiltar gundumar Mashio, inda daga bisani ya zama mataimakin shugaban karamar hukumar.
A kokarinsa na cigaba da karatunsa, sabon Kakakin ya garzaya inda yayi Diploma a Ramat Polytechnic Maiduguri, da Digirinsa na farko a Jami’ar Maiduguri a fannin kimiyyar siyasa.
Mashio ya tsaya takarar dan majalisar dokokin jihar Yobe mai wakiltar mazabar Jajere a 1999, ya yi aiki a kwamitoci da mukamai daban-daban a zauren majalisar.
Sauran manyan kusoshin majalisar sun hada da mataimakin Kakakin majalisar, Hon. Yau Usman Dachia, Shugaban Majalisar, Hon. Nasiru Hassan Yusuf, Mataimakinsa, Hon. Hassan Muhd ​​Yusufari, Mai.Tsawatarwa a zauren majalisar, Hon. Muhammed Auwal Isa Bello, mataimakinsa, Hon. Ahmed Musa Dumbu.
A jawabinsa na godiya, sabon Kakakin majalisar, Chiroma Buba Mashio ya bayyana jin dadinsa ga takwarorinsa bisa ga damar da suka bashi ya jagoranci zauren majalisar na 8, tare da daukacin al’ummar jihar baki daya.
Mashio ya yi alkawarin samar da ingantaccen shugabanci “ba tare da nuna son kai ba; tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya zai jagorance ni. Zan aiwatar da manufar bude kofa don maraba da shawarwari don inganta shugabanci nagari don samar da ingantacciyar doka.
Shugaban majalisar ya bada tabbacin yin aiki cikin kwanciyar hankali da bangaren zartaswa da bangaren shari’a domin a samar da shugabanci nagari a jihar Yobe.