Kotun Ƙoli ta bayyana cewa zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a Jihar Rivers a ranar 5 ga Oktoba, 2024, ba shi da inganci, kuma ya saɓa wa doka. Kotun ta yanke hukuncin cewa zaɓen ya kasance haramtacce, kuma saboda rashin bin ƙa’idojin da doka ta tanada kafin gudanar da irin wannan zaɓe.
A cewar kotun, hukumar zabte ta Jihar Rivers (RSIEC) ta karya dokokin gudanar da zabe, inda ta saɓa wa sashi na 150 na dokar zaɓe ta 2022.
A baya dai, wata babbar kotu a Abuja ta hana hukumar zabe ta ƙasa (INEC) bayar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a ga RSIEC domin gudanar da zaɓen, bisa hujjar cewa ba a cika sharuɗɗan gudanar da zaɓe ba. Haka kuma, kotun ta hana Sufeto Janar na ‘Yansanda da hukumar tsaro ta DSS samar da tsaro yayin zaɓen, domin gujewa duk wata matsala da ka iya tasowa. Wannan umarni ya biyo bayan ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar, tare da rakiyar lauyoyinta Joseph Daudu, Sebastine Hon, da Ogwu James Onoja, dukkaninsu SAN.
- Shugaban NPA Ya Kai Ziyarar Neman Masu Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Onne Da Ta Jihar Ribas
- Jam’iyyar APC Ta Sahalewa Shugaba Tinubu Damar Neman Shugabancin Nijeriya A 2027
Kotun ta bayyana cewa RSIEC ta yi kuskure wajen sanya ranar zaɓe ba tare da bin dokokin da suka wajaba ba, ciki har da rashin sanar da jama’a kwanaki 90 kafin a gudanar da zaɓen, kamar yadda doka ta tanada. Haka kuma, an gaza sabunta da tantance rajistar masu kaɗa kuri’a, wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar zaɓe. Saboda haka, kotun ta ayyana cewa zaben bai cika ƙa’idojin doka ba, kuma ba za a amince da sakamakonsa ba.
Bugu da ƙari, kotun ta haramta amfani da rajistar masu kaɗa ƙuri’a da INEC ta tanadar, har sai an cika dukkan sharuddan da doka ta tanada. Wannan hukunci na kotu yana nufin cewa duk wanda aka zaɓa a ƙarƙashin wannan zaɓe ba zai ci gaba da riƙe muƙaminsa ba.
Wannan mataki yana da matuƙar tasiri a siyasar Jihar Ribas, inda jam’iyyar APP ce ta lashe mafi yawan kujeru a zaɓen da aka soke.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp