Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ta amince da daukar dan wasan gaba Vitor Roque mai shekaru 18 daga kungiyar Athletico Paranaense ta kasar Brazil.
Ya rattaba hannu akan wata yarjejeniya wadda za ta fara a shekara ta 2024, kuma za ta yi aiki na tsawon shekaru bakwai.
- Zan Bude Sabon Shafi A Barcelona, Cewar Gundogan
- Bousquets Ya Koma Inter Miami Bayan Barin Barcelona
Daga ciki akwai yarjejeniayr da ta hada da batun Yuro miliyan 500 (£427m) ga duk mai son daukar dan wasan kwantiraginsa bai kara ba.
Roque ya zura kwallaye 22 a wasanni 66 da ya buga wa Paranaense, kuma ya zama matashin dan wasa na farko mai karancin shekaru da ya bugawa kasar Brazil kwallo a watan Maris.
Roque ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa “na yi matukar farin cikin kulla yarjejeniya da Barca mafarki na ne ya zama gaskiya.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa zakarun na Sifaniya za su biya Yuro miliyan 30 (£25.6m) kan matashin dan wasan, tare da wani Yuro miliyan 31 (£26.4m) na tsarabe tsarabe.
Roque ya kare ne a matsayin wanda ya fi zura kwallo a raga a gasar Kudancin Amurka ta matasa ‘yan kasa da shekara 20 a farkon wannan shekarar da kwallaye shida yayin da Brazil ta lashe kofin karo na 12.
Ya kuma taimaka wa Paranaense zuwa wasan karshe na Copa Libertadores a bara.