Ko mai ya faru, Hukumomin Saudiyya suka soke bizar dukkan fasinjoji 264 da aka yi jigilarsu zuwa Jeddah daga Kano a ranar Lahadi?
Hukumomin kasar Saudiyya sun tubure cewa, lallai jirgin sai ya mayar da dukkan fasinjojinsa zuwa inda ya ta so (Nijeriya).
- NIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Jami’anta 4, 7 Sun Ji Rauni A Wani Hadarin Mota A Kano
- Buhari Ya Taya APC Murnar Nasarar Lashe Zaben Gwamnoni A Jihohin Imo Da Kogi
Jirgin ya taso ne daga filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas zuwa filin jirgin Mallam Aminu Kano da ke Kano a daren Lahadi ya sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jeddah a kasar Saudiyya.
Amma abin da ya ba ma’aikatan kamfanin jirgin mamaki, hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa, an soke dukkan bizar fasinjojin.
Kuma duk da cewa, Fasinjojin an tantance su da irin tsarin na’urar zamani ta tantance fasinja (APIS) a Nijeriya kuma a gaban hukumomin Saudiyya da ke sa ido a filin.
Daily trust ta ruwaito cewa, kamfanin jirgin Air Peace a makon da ya gabata ne ya kaddamar da jigilar fasinja kai tsaye zuwa Jeddah wanda ake kamanta hakan da tsarin daukar kaya mai nauyi ga kamfanin.
An tattaro cewa, a lokacin da ofishin jakadancin Nijeriya ya gana da hukumomin Saudiyya, kasar ta amince da wasu fasinjojin amma ta dawo da 177 daga cikin 264.