Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar Talata, ya iso filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga birnin Landan na kasar Birtaniya (UK).
Shugaba Buhari ya bar Nijeriya ne a ranar 3 ga watan Mayu zuwa kasar Birtaniya domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles III da Sarauniyarsa, Camilla, ta kasar Birtaniya.
Shugaban wanda tun farko aka shirya zai dawo Abuja cikin mako guda, sai ya sake tsawaita dawowarsa na tsawon mako guda sakamakon shirya ganin likitan hakoransa domin duba lafiyarsu.
A wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da zama a birnin Landan na kasar Birtaniya na tsawon mako guda, sabida ganin likitan hakoransa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp