Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya dawo Nijeriya kwanaki takwas gabanin rantsar da shi.
Jigogin jam’iyyar APC ne suka tarbi Tinubu a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
- Shugabannin Kasashen Tsakiyar Asiya Sun Yi Alkawarin Kara Hadin Gwiwa Da Sin
- Amurka Ta Bukaci Aiki Tare Da Sabuwar Gwamnatin Tinubu
Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Tunde Rahman, ya bayyana cewa, kwanaki 10 da suka gabata, dan takarar jam’iyyar APC ya bar kasar nan zuwa Turai domin ganawa da masu zuba jari da kuma shirye-shiryen mika mulki.
Zababben shugaban kasar ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, a lokacin da yake a Turai.
Sai dai wannan ganawa ta bar baya da kura, inda wasu a jam’iyyar APC ke guna-guni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp