Gwamnonin jam’iyyar PDP biyar da aka fi sani da PDP G-5 a karkashin jagorancin gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, sun yi alkawarin marawa gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed baya domin samun wa’adi na biyu a zaben badi.
Kungiyar ta bayyana goyon bayan ta ga gwamnan Bauchi a ranar Laraba yayin wata ziyara da suka kai Bauchi domin nuna goyon baya ga gwamna Mohammed.
- Dan Wasan Senegal Mane Ba Zai Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ba Saboda Rauni
- 2023: Atiku da Gwamnan Bauchi Sun Sasanta Rikicin Da Ke Tsakaninsu
Idan dai za a iya tunawa, gwamnan Jihar Bauchi ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da hada kai da wasu gungun ‘yan siyasa na jihar domin dakile yunkurinsa na sake tsayawa takara a 2023.
Sai dai dukkansu sun warware sabanin da ke tsakaninsu tare da yanke shawarar yin aiki tare domin samun nasarar zabe a 2023 bayan wani taro da suka yi a Abuja a daren ranar Talata.
Sai dai da yake magana a madadin Gwamnonin G-5 a gidan Ramat da ke Bauchi, Gwamna Wike ya ce duk abin da ya shafi Gwamna Bala Mohammed shi ma ya shafe su a kungiyance, don haka sun kuduri aniyar goyon bayan takararsa a karo na biyu.
Ya ce duk da cewa gwamnan Bauchi ya yi kyakkyawan aiki ta yadda al’ummar jihar za su zabe shi a zaben gwamna na 2023, amma suna ganin goyon bayansu a wannan mawuyacin lokaci na da muhimmanci ga gwamnan.
“Ba mu sake tsayawa takara karo na biyu ba duk da cewa wasunmu na neman tikitin ‘yan majalisar dattawa a jihohinsu, ni kadai ne ban tsaya takara ba bayan faduwa zaben fidda gwani na shugaban kasa,” in ji Wike.
Da yake mayar da martani, gwamnan Jihar Bauchi, ya ce goyon bayan da gwamnonin G-5 suke ba shi a wannan lokaci da jam’iyyar ke fuskantar kalubale ya ji dadi.
Sai dai ya yi mamakin dalilin da ya sa ba a mayar da shi cikin tawagar PDP G-5 tun daga farko ba.
“G-5 Gwamnonin sun kore ni ne saboda wasu dalilai da suka fi sanin su. A siyasa sai ku tafi tare da mutanen da kuke da abin da ya kamance da su.” In ji Mohammed.
Gwamnonin G-5 da suka hada da Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu na Jihar Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da Samuel Ortom na Jihar Benue a halin yanzu suna ganawar sirri da gwamna Mohammed yayin da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, bai bayyana ba.
LEADERSHIP ta rawaito ganawar ta zo ne a daidai lokacin da aka sasanta tsakanin Gwamna Mohammed da Atiku Abubakar a daren ranar Talata a Abuja.