Hukumomin tsaron Nijeriya sun tabbatar da tashin bama-bamai A Maiduguri, inda wata ‘yar kunar-bakin-wake ta tarwatsa kanta.
Harin ya faru ne a Masallacin Zannari kan titin Dikwa zuwa Maiduguri, yayin da nan ta ke ta kashe mutum takwas.
An dai kai harin ne lokacin sallar Asuba a safiyar yau Litinin wasu mutum 15 kuma sun jikkata a harin.
Wasu rahotanni sun ce jami’an tsaro na bin ‘yar kunar bakin waken da ke kokarin tserewa ne a lokacin da ta tayar da bam din da ke jikinta.