‘Yar wasan Super Falcons, Michelle Alozie, ta tabbatar da cewa tana lafiya duk da abinda yar wasan Ingila Lauren James.
Ta yi mata a wasan zagaye na 16 tsakanin Nijeriya da Ingila a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a ranar Litinin.
An dai bai wa Lauren James jan kati ne a minti na 87 da fara wasa, bayan da ta taka Alozie da gangan.
Da farko dai an nuna wa James katin gargadi amma bayan tantancewar VAR, alkalin wasa ta sauya hukuncin kuma ta kore ta.
Bayan wasan, Alozie ta tabbatar da cewa tana cikin koshin lafiya bayan takin James kuma ta tabbatar da cewa ba ta da wani fushi a kan tauraruwar Ingila.
Da ta ke magana da manema labarai, Alozie ta ce, Lauren kwararriyar ‘yar wasa ce kuma ta yi mamakin abin da ta yi har yasa aka kore ta daga wasan.
Super Falcons dai sun yi fafutuka sosai wajen ganin sun rike Lionesses babu ci amma daga karshe suka tashi 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida sannan suka fice daga gasar cin kofin duniya ta mata.