Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Yarinya mai shekara bakwai, Maryam Isah daga karamar hukumar mulki ta Fakai a Jihar Kebbi da aka gano cewa tana da cututtuka na ‘Cyanotic’ ga zuciyarta , tana neman kimanin Naira Miliyan uku da Dari biyar (N3.5 Million) don gyara yanayin rashin lafiya a asibiti Indiya.
Maryam Umar Isah ita ce ‘ya ta hudu wurin iyayenta. An gano cutar ciwon zuciyar ne a Cibiyar bincike na kananan yara da ke Asibitin Jami’ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sakkwato .
A wata takardar likita, ta tabbatar da kamuwa da cutar ga Maryam Umar; takardar da Dakta Usman M. Sani ya rattaba wa hannu.
“Pulse Odymeyry ya nuna jigilar kwayoyin cutar halitta na 78% na a cikin zuciyar Maryam.
Hakazalika, wata takardar likita daga Ofishin Jakadancin Madras, Indiya da Dokta K Sibakumar ya sanya wa hannu don tabbatar da rashin lafiyar ita Maryam ta cutar ciwon zuciya mai rame a cikin zuciyar. Inda ya ce zai iya yi mata aikin zuciyar amma a asibitin su da ke kasar indiya.
Yayin da yake magana da manema labarai a Birnin Kebbi, mahaifin Maryam, Malan Umar Isah ya bayyana cewa an gano tana wannan cutar ne tun daga shekarar 2012 a lokacin da ta kasance shekarua uku da rabi kuma likitoci sun ce ana iya maganin cutar ta zuciya. Amma yanzu ne cutar ke tsana ni.
Ya yi kira ga jama’a da gwamntin jihar ko ta tarayya don taimakawa yariyarsa Maryam kan ciwon zuciya da ta shafe kiminin shekara hudu tana fama da wannan rashin lafiya. Domin samun lafiyar Maryam.
Za a iya neman mahaifi Maryam a kan wannan adireshi domin taimaka wa ga ‘yar tasa; Cibiyar Samar da makamashi mai sabuntawa ta kwalejin tarayya ta Waziri Umar da ke a Birnin-kebbi ko kuma a neme shi ta lambar waya kamar haka 08060546920.