Connect with us

LABARAI

‘Yar Takarar Gwamnan Bauchi Ta Gargadi Jama’a Kan Sayar Da Kuri’u

Published

on

‘Yar takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar (ACD) Hajiya Baheejah Mahmood Abdullahi ta gargadi masu zabe dangane da sake saida kuri’unsu kan kudi kankani ga ‘yan siyasa a babban zaben 2019 da ke tafe.
Baheejah ta yi gargadin ne a karshen mako a Bauchi a lokacin da ta amshi bakwancin wasu gungun mata, “ya kamata ku kaurace wa amsar kudi ko wani abu domin saida ‘yancinku na kuri’u ga wasu ‘yan siyasar. ya dace ku yi zabi da kanku ba wai wani ya baku taro sisi ya sanyaku ku zabi wani da yake da maradi ba. ta fuskacin sayar da kuri’u ba za a taba samun nagartattun jagogori ba, domin duk wanda zai cire kudi ya sayi kuri’a ta bai yarda da kansa da nagartarsa bane,”
Ta kara da cewa, “muddin wani dan siyasa ya yi nasara ta hanyar sayan kuri’u daga wajen jama’a, ba aiki zai yi musu ba domin saye ya yi, don haka muna son jama’an jihar nan su samu aiki mai nagarta don haka dole ne a kauce wa sayar da kuri’u. illolin sayar da kuri’u suna da yawa, idan wanda ya sayi kuri’u a wajen mutane ya samu nasara yana shiga ofis ba zai taba yaki da cin hanci da rashawa ba, illa ma ya kara mata armashi,” Inji ta
Baheejah ta kuma shaida cewar ya kamata a kawo karshen amfani da kudi ta fuskacin siyasa gaba daya domin a cewarta ta hakan ma za a iya kawo karshen cin hanci da rashawa.
Ta kuma bayyana cewar tana da tabbacin samun kwari guiwa daga wadanda suka dace, tana mai shaida cewar shugaban kasa Buhari da matarsa za su dafa wa mata ‘yan siyasa domin su ma su samu shiga ana dama da wasu, don haka ne ta nuna gayar tsammaninta na kasancewa gwamnan jihar Bauchi a 2019.
Hajiya Baheejah Mahmud, ta kuma yi amfani da wannan damar wajen bayyana cewar mata da matasa suna da gagarumar rawar takawa wajen ciyar da kasar nan gaba, don haka ne ta nemi masu zabe su yi amfani da damarsu ta yin zabe wajen zabar mata a kujeru daban-daban domin suma su bayar da tasu gudunmawar wajen gina kasa.
Shugaban jam’iyyaar ACD El-Faruk Gado ya shawarci mata da su shiga cikin jam’iyyar ACD a cewarsa korarfu ga mata a bude take don neman kujeru daban-daban a jihar Bauchi, ya kuma shaida cewar za su mara wa mata baya domin su kai ga nasarar cimma muradinsu. El-Faruk ya kara da cewar,

Advertisement

labarai