Daraktan Hukumar Kula da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki ta Kasa (NACA), Dakta Temitope Ilori, ta bayyana damuwa game da karancin matakan kariya daga cuta mai karya garkuwar jiki daga uwa zuwa jariri a Nijeriya.
Ta ce adadin rage kamuwar bai wuce kashi 33 ba, yayin da ake da burin cimma kashi 95 na dakile yaduwar cutar.
- Gwamnatin Kebbi Ta Dakile Yunkurin Lakurawa Na Satar Shanu
- Netanyahu Ya Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Hezbollah
Ta ce kimanin yara 160,000 masu shekaru kasa da 14 suna dauke da cutar a Nijeriya kamar yadda rahoton UNAIDS na 2023 ya nuna.
Yayin jawabinsta a Abuja gabanin ranar cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya ta 2024, wacce aka yi wa taken “Nemo Hanya: Ci Gaba da Yakar Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki, Dakile Dakile Ta A Tsakanin Yara A Nijeriya Zuwa 2030.”
Ta ce Nijeriya na da kashi 1.4 na masu cutar tsakanin mutanen da shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 64, tare da kimanin mutane miliyan biyu da ke fama da cutar.
A duk shekara, Nijeriya na samun sabbin mutane 22,000 da ke kamuwa da cutar, tare da mutane 15,000 da ke mutuwa saboda cututtukan da suka shafi cuta mai karya garkuwar jiki.
Domin magance wannan matsala, an kafa kwamiti na kasa don tabbatar da cewa babu wani jariri da aka haifa da cutar.
Kazalika, an kafa kwamitocin jihohi domin tallafa wa wannan mataki.
Dakta Ilori ta jaddada kudirin NACA na ci gaba da yakar cutar duk da rashin samun tallafi daga masu bayar da gudunmawa.
Ta kuma ce akwai shirye-shiryen da gwamnati ke jagoranta don tabbatar da tsaro a bangaren kiwon lafiya da zamantakewa a nan gaba.