Turawan mulkin mallaka sun dawo da hedikwatar su zuwa kaduna daga Zungeru (Dungurum) a 15 ga watan Nuwamban 1916.Yau Talata 15 ga watan Nuwamba, 2022, Kaduna ta cika shekaru 105 da kafuwa.
Gwamnatin mulkin mallaka, ta taso zuwa kaduna a ranar 15 ga watan nuwamban 1916, sai daga bisani sauran ma’aikatun dake karkashin turawan suka fara biyo hedikwatar zuwa Kaduna.
Ma’aikatar Fidaburdi a ranar 26 ga watan Nuwamba suka taso, sai ma’aikatar Safiyo da Baitulmali da sakatariya suka iso a karshen shekara, daga nan kuma sai ma’aikatar lafiya da ta jami’an ‘yan sanda.
A cikin shekaru hudu kacal aka kammala manyan gine-gine a jihar Kaduna. An yi wadannan gine ginen ne cikin rahusa, sabida arhar aikin lebura da turawan suka samu. An kashe fam 116,150.00 wajen gina garin kaduna kafin a tare baki daya.
Turawan Mulkin Mallaka karkashin jagorancin Gwamna Luggard sun kafa Garin Kaduna don ta zama hedikwatar Nijeriya.
Tun daga Gwamna Luggard, wanda shi ne gwamnan kaduna na farko, garin Kaduna ya samu gwamnoni da dama, daga cikin su akwai:
- Abba Kyari Daga 28 May 1967 zuwa Jul 197
- Usman Jibrin daga July 1975 zuwa 1977
- Muktar Muhammed daga 1977 July 19
- Ibrahim Mahmud Alfa daga July 1978 zuwa October 1979
- Abdulkadir Balarabe Musa daga October 1979 23 zuwa Jun 1981
- Abba Musa Rimi daga 6 July 1981zuwa October 1983
- Lawal Kaita daga October 1983 zuwa Decem 1983
- Usman Mu’azu daga January 1984 zuwa. August 1985
- Dangiwa Umar daga August 1985 zuwa June 1988
- Abdullahi Sarki Mukhtar daga July 1988 zuwa August 1990
- Abubakar Tanko Ayuba daga August 1990 2 zuwa Janu 1992
- Mohammed Dabo Lere daga 2 January 1992 zuwa Novem 1993
- Lawal Jafaru Isa daga 9 December 1993 22 zuwa Aug 1996
- Hammed Ali daga 22 August 1996 zuwa August 1998
- Umar Farouk Ahmed daga August 1998 zuwa 29 May 1999
- Ahmed Makarfi daga 29 May 1999 zuwa 29 May 2007
- Mohammed Namadi Sambo daga 29 May 2007 zuwa 19 May 2010
- Patrick Ibrahim Yakowa daga 20 May 2010 zuwa 15 Decem 2012
- Mukhtar Ramalan Yero daga 15 December 2012 zuwa 29 May 2015
- Nasiru Ahmed El- Rufai daga 29 May 2015
Daga shafin Facebook na Kasar Zazzau Jiya da Yau