Connect with us

MANYAN LABARAI

Yau Ake Sa Ran ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa Zasu Rufe Yakin Neman Zabensu

Published

on

A yau Alhamis ake sa ran kammala yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Tarayyar Nijeriya kamar yadda dokar zaben kasar ta tanada, yayin da manyan ‘yan takarar shugabancin kasarnan, Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP suka karade lungu da sako na sassan kasarnan da zummar neman kuri’un jama’a.

Jam’iyyar APC mai mulki za ta kammala yakin neman zabenta ne a jihar Katsina a yau Alhamis bayan ta gudanar da gangaminta a jiya Laraba a birnin tarayya Abuja, ko da yake shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da madugun jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba su samu damar halartar gangamin ba.

Ana rade-radin cewa, PDP za ta gudanar da nata gangamin wani lokaci a yau a birnin Abuja, amma babu wata kwakkwarar majiya daga bangaren jam’yyar da ta tabbatar da wannan rahoton.

Amma wadansu rahotanni sun nuna cewa; tun a jiya aka zaci cewa, PDPn za ta yi gangamin nata a Abuja, amma ya ci karo da na APC mai mulkin kasar. Sai ta dage zuwa wani lokacin.

A jibi Asabar, ake saran kimanin mutane miliyan 84 za su halarci rumfunan zabe a sassan kasar domin kada kuri’unsu ga wanda suke fatan kasancewa shugaban Nijeriya a shekarar 2019.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: