Khalid Idris Doya" />

Yau Da Karfe 6 Na Yamma Za A Bude Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe —Shugaban INEC

•Masu Sa-ido 73,000 Ne Za Lura Da Zaben
•An Samar Da ‘Yan Sandan Da Za su Tabbatar An Yi Zabe Lafiya —Mukaddashin Sifeton ‘Yan Sanda

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa, yau Asabar 23, ga watan Fabarairu na shekara ta 2019, da misalign karfe 6:00ny za a bude cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a babbar gudanar da tarurruka da ke Abuja. Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa manema labarai jiya Juma’a a Abuja.
Haka kuma ya ce, mutum 73, 000 ne masu sa-ido a harkar zabe za su lura da yadda wannan zaben zai gudana a fadin kasar nan.
Ranar ta yau ta kasance rana ce, da al’ummar Nijeriya da ma na sauran kasashe ke burin ganinta, domin kuwa rana ce wadda take ta tarihi a kasar nan.
A wannan ranar ta yau ce miliyoyin ‘yan Nijeriya suka yiwo fitar dango domin zabar wanda zai shugabnci kasar nan na tsawon shekara hudu masu zuwa, tare da ‘yan majalisar wakilai da na dattijai.
Ya rage sauran a wanni a fara wannan zabe ‘yan takarar shugaban kasa daga jam’iyya daban-daban suka janye takarar ta su, yayin da suka mince su goya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.
In dai za iya tuna wad a Hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya cewa Asabar din makon jiya za a yi wannan zabe, ammam wasu dalilai masu karfi suka sa dole aka dage zuwa yau din nan, wanda kuma a halin yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da gudanar da zabensu kamar yadda aka tsara.
Mukaddashin Babban Sifeton ‘yan sanda ya tabbatarwa da al’ummar Nijeriya cewa, sun tanaji ‘yan sandan da za su kula wannan zabe, cikin ikon Allah kuma a yi a gama lafiya.

Exit mobile version