Abba Ibrahim Wada" />

Yau Za A Cigaba Da Buga Wasannin Laliga

La Liga

A yau Talata za a ci gaba da buga wasannin La Liga na kasar Spaniya, karawar mako na 19 da za a yi wasanni uku kuma an buga wasan karshe a gasar Spanish Super Cup tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao a filin wasa na Sebilla wasan da Bilbao ta samu nasara daci 3-2 kuma aka bawa Messi jan kati..

Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga, ita kuwa Bilbao tana ta 12 a kasan teburi sai kuma Atletico Madrid wadda keda kwantan wasa biyu, ita ce kan gaba a teburi da maki 41, sai Real Madrid ta biyu mai maki 37.

Kawo yanzu an buga wasanni 177, amma wasu kungiyoyin suna da kwantan wasa da aka kai fafatawar mako na 18, an kuma ci kwallo 427, Barcelona ce kan gaba mai kwallaye 37 a raga kawo yanzu .

Lionel Messi kyaftin din Barcelona shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Spaniya mai kwallaye 11 a raga, Gerard Moreno dan wasan Billarreal shi kuma ya zura kwallaye 10 a raga, sai Iago Aspas na kungiyar Celta Bigo da kuma Luis Suarez na Atletico Madrid da kowanne keda kwallaye tara-tara a raga.

Kawo yanzu wasan da aka ci kwallaye da yawa a gida shi ne wanda Atletico Madrid ta doke kungiyar Granada da ci 6-1 ranar 27 ga watan Satumbar 2020 wasan da har yanzu ba’a samu wanda akaci kwallaye kamarsa ba.

Fafatawar da kungiyar waje ta je ta ci kwallaye da yawa shi ne wanda Billareal ta je ta doke Celta Bigo 4-0 ranar 8 ga watan Janairun shekarar nan ta 2021 da wanda Barcelona ta je gidan Granada ta yi nasara da ci 4-0 ranar 9 ga watan Janairun 2021.

Wasannin mako na 19 za a fafata a gasar La Liga.

Ranar Talata 19 ga watan Janairu

Real Madrid vs Elche

Cadiz vs Lebante

Deportibo Alabes vs Sebilla

Ranar Laraba 20 ga watan Janairu

Getafe vs Huesca

Real Betis vs Celta Bigo

Billarreal vs Granada

Ranar Alhamis 21 ga watan Janairu

Balencia vs Osasuna

Eibar vs Atletico Madrid

Lebante vs Real Balladolid

Huesca vs Billarreal.

Exit mobile version