Manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke buga gasar Firimiya ta kasar Ingila Manchester United da Chelsea za su kece raini a filin wasa na Old Trafford da ke Manchester a wasan mako na 10 na gasar.
Zuwa yanzu Chelsea ce ke matsayi na 6 da maki 17 a teburin gasar yayin da Manchester United wadda ta kori kocinta a makon da ya gabata ta ke matsayi na 13 da maki 11 kacal.
Manyan kungiyoyin biyu sun buga wasanni sau 193 a tarihi, wanda Manchester United ta ke gaba a samun nasara bayan doke Chelsea sau 77, aka yi canjaras 61 sai Chelsea ta samu nasara sau 55.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp