ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Kasashen Yamma Za Su Iya Daukar Nauyin Da Ke Bisa Wuyansu

by CMG Hausa
3 years ago
Kasashen yamma

Kwanan baya, an gudanar da taron kolin kasashen Afirka game da daidaita matsalar sauyin yanayi a birnin Rotterdam na kasar Netherlands, inda shugabannin kasashen Afirka guda shida suka hallara, a yayin da firaministan kasar Netherland shi kadai ya halarci taron, ba tare da shugabannin sauran kasashen yamma da aka ba su goron gayyata ba, ciki har da Faransa da Norway da Canada da sauransu.

Hakan ya bakanta ran shugabannin kasashen Afirka. Shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shi ne shugaban karba karba na kungiyar tarayyar Afirka, ya furta a wajen bikin bude taron cewa, “Abin bakin ciki shi ne, na lura da rashin hallarar shugabannin kasashe masu ci gaban masana’antu a wajen taron.

  • Sin Da Afirka Sun Zamo Manyan Abokan Tafiya A Tafarkin Wanzar Da Ci Gaba

Na yi zaton idan mun yi kokari mun bar Afirka har mun zo Rotterdam, to, mutanen kasashen Turai da sauransu za su fi samun saukin halartar taron.” Shugaban jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, shi ma ya yi suka cewa, “Sanin kowa ne su ne suka fi lalata yanayin duniyarmu.”

ADVERTISEMENT

Abun hakan yake, kafin kasashe masu tasowa suka fara raya masana’antu, tuni masana’antun kasashe masu sukuni na yammacin duniya suka fara fitar da iska mai gurbata muhalli a shekaru kusan 200 da suka wuce.

Dan tasiri kadan ne kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa suka haifar ga sauyin yanayin duniya, amma illolin da sauyin yanayin ke haddasawa sun fi addabarsu.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

A sabo da haka, kasashen duniya sun cimma yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da ma yarjejeniyar Paris, wadanda suka bukaci kasashe masu ci gaba su dauki matakai na kayyade iskar Carbon da suke fitarwa, tare kuma da samar da kudade da ma fasahohi ga kasashe masu tasowa wajen daidaita matsalar. Sai dai abin takaici shi ne, ba a aiwatar da yarjejeniyoyin yadda ya kamata ba, kuma kasashen Turai da Amurka ma sun gaza cika alkawuransu, na taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi.

Rashin hallarar shugabannin kasashen yamma a wajen taron, ya shaida yadda suke rashin girmama kasashen Afirka a kullum, baya ga kuma yadda suke gudun daukar nauyin da ke bisa wuyansu. Ba kawai sauyin yanayi na shafar makomar kasashen Afirka ba ne, har ma yana shafar makomar bai daya ta ‘yan Adam da ta duniyarmu baki daya.

Kamar dai yadda Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren MDD ta bayyana a wajen taron, “da fika-fikai biyu ne tsuntsu ke iya tashi”, dole ne kasashen Yamma su gane cewa, makomar dan Adam daya ce, kuma su cika alkawuran da suka dauka, tare da daukar nauyin da ke bisa wuyansu, ta fannin daidaita matsalar sauyin yanayi.”(Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Biyayya Ga Umarnin Allah Ne Kadai Zai Kawo Karshen Matsalolin Nijeriya —Sheikh Yusuf Ali

Biyayya Ga Umarnin Allah Ne Kadai Zai Kawo Karshen Matsalolin Nijeriya —Sheikh Yusuf Ali

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

December 22, 2025
An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.