A yadda wasanni suke tafiya tabbas kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta kama hanyar lashe gasar Premier na bana in dai ba wani gagarumin sammatsi ba – bayan da ta kara kankane matsayinta na daya a tebur da tazarar maki 13, wanda hakan ya nuna kungiyar ta nufi hanyar lashe kofin da aka yi zaton Manchester City ko Arsenal daya a cikinsu ne zai lashe a kakar ta bana.
Idan muka duba tarihi babu wata kungiya a tarihin babbar gasar ta Ingila, tun daga kakar wasa ta 1888 zuwa 1889, da ta taba yin wannan fintinkau a wannan mataki na gasar kuma a ce ba ta dauki kofin ba kuma a halin yanzu ma Liberpool din tana kan ganiyarta na lashe wasa ga duk kungiyar da ta hadu da ita a hanya. Tsohon dan wasan Ingila, Gary Lineker ma cewa ya yi, “Abin ya fara tashi daga gasa ya zama tamkar.
tattaki ko ba haka ba ne?” Duk tsawon wannan kakar Liberpool ta yi rashin nasara ne sau daya kawai a gasar ta Premier.
Mai bi mata a baya-a baya, kungiyar Arsenal ta zubar da maki a dukkanin wasanninta biyu na baya-bayan nan ciki har da wanda ta yi canjaras ba ci da Nottingham Forest da kuma rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta West Ham United har gida. Amma kociyan kungiyar ta Liberpool Arne Slot ya ce: “Har yanzu da sauran tafiya, wasa 10 ba nan ba ne…
Ya ce “Yanzu ‘yanwasan suna da hutu, daga nan za mu mayar da hankali kan wasanmu na Zakarun Turai da Paris St-Germain fiye da yadda muka mayar da hankali a kan teburin Premier,” in ji kociyan. Amma Ko kociyan Arsenal Mikel Arteta, yanzu dole ya san cewa kusan kasuwa ta riga ta ci ta cinye – ta tashi – to amma kafin wasansu da Forest ya ce shi bai sallama ba – bakin rai bakin fama.
Bayan wasan na Forest, Mikel Arteta ya gaya wa manema labarai cewa – haka abin yake ba bambanci mako daya baya, da mako biyu baya, da ma wata uku baya. Ya ce abin kawai da za su yi yanzu shi ne su tabbatar suna cin wasanninsu su ga maki nawa za su samu – kenan dai har yanzu, Artetan bai sallama ba – yana ganin cinta duk da tazarar da ke tsakaninsu da Liberpool din.
To amma tsohon danwasan gaba da gefe na Liberpool Stebe McManaman, ya ce ai babu wata tantama ba wata tababa Liberpool a wannan kadami tamkar wani ingarman doki ne da ya kama hanyar cin gasa ba mai shiga gabansa sai dai a hangi kurarsa kuma duk sauran kungiyoyin sai zubewa suke suna taimaka wa Liberpool din.
Kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest na ta uku a tebur da bambancin maki shida a bayan Arsenal, ita ma kuma Manchester City – wadda sau hudu tana cin kofin na Premier a jere – na bayan Forest din da maki daya wanda hakan ya nuna irin bajintar da kungiyar Forest ta nuna karkashin kociyanta dan Portugal, Nuno Espirito Santos, wanda a baya ya taba koyar da Wolbes.
A tarihi kungiya daya ce kawai ta taba wannan fintinkau da maki 13, kuma ba ta dauki kofin na Premier ba – lokacin da kiri-da-muzu Manchester United na ji tana gani kuma Arsenal ta yi gaba da kofin a kakar 1997-98 – to amma wannan tun a farkon kakar ne Utd din ta bayar da tazarar da ta zama tamkar sammakon-bubukuwa.
Wanne Lokaci Liberpool Za Ta Zama Zakara?
Ba zai zama riga-mallam-masallaci ba a ce kungiyar Liberpool ta zama zakarun Premier masu jiran-gado a yanzu – magana ce kawai ta yaushe amma ba idan har ba domin kamfanin kididdiga kan harkokin wasanni na Birtaniya- Opta- ya ce akwai yuwuwa kashi 98.7 cikin dari Liberpool ce za ta dauki kofin na Premier, yayin da Arsenal ke da dama ta kashi 1.3 cikin dari.
Liberpool ta yi wa Arsenal fintinkau da tazarar maki 13, yayin da ya rage wasa 10 a kammala gasa – koda yake Arsenal na da ragowar 11, sannan idan har Liberpool ta ci gaba da wannan tazara ta maki 13, wannan zai sa ta ci kofin da ragowar wasa hudu a nade tabarmar gasar – ranar 26 ga watan Afirilu kenan a wasanta da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham.
To amma idan Arsenal ta ci kwantan wasanta daya ta kuma yi daidai da sauran sakamakonta to Liberpool, za ta dauki kofin a karshen mako mai zuwa a wasanta da Chelsea. Idan har haka ta tabbata wasansu na farko a matsayin zakarun Premier zai kasance a gida da Arsenal, wadda za ta iya musu rakiyar shiga fili a matsayin zakaru, wanda a tarihi haka ake yi.
Saboda ci gaban da suke samu a gasar Zakarun Turai da kuma matsayinsu a gasar kofin Carabao na wasan karshe da Newcastle da kuma hutun da za a iya na wasannin kasashe, Liberpool za ta yi wasa daye ne kawai na Premier a watan Maris kuma lokaci mafi kusa da Liberpool za ta iya daukar kofin na Premier a kididdiga shi ne makon farko na Afirilu.
Idan Liberpool din ta ci wasanninta uku na gaba kuma aka doke Arsenal a wasanninta hudu na gaba kuma kungiyoyin da ke bayansu suma suka zubar da maki ‘yan kalilan, to Liberpool za su zare kofin ranar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp