Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League.
An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga.
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
- Ballon D’or: An Zaɓe Ni Ne Kamar Yadda Aka Zaɓe Ka – Martanin Rodri Ga Ronaldo
Goncalo Ramos wanda ya maye gurbin Cristino Ronaldo ne ya jefa ƙwallo ta biyar a ragar Denmark gab da za a tashi daga wasan, a wasan farko da ƙasashen su ka buga a ranar Alhamis, Denmark ce ta doke Portugal da ci ɗaya mai ban haushi.
Kafin a tashi wasan dai an karrama ɗan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva da kyautar girmamawa kasancewarshi ɗan wasa na 8 a tarihin ƙasar Portugal, da ya buga wasanni 100 a tawagar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta maza, tawagar Roberto Martinez za ta kara da Jamus a wasan gaba, bayan da tawagar Julian Nagelsmann ta doke Italiya da ci 5-4 a wasanni biyu da su ka buga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp