Tun bayan komawar dan wasa Kylian Mbappe Real Madrid masu sharhi suka dinga hasashen irin gudunmawar da dan wasan zai iya ba wa kungiyar kasancewarsa kwararre wajen iya jefa kwallo a raga da kuma iya sarrafa kwallo.
Kawo yanzu dai sabon dan wasan da Real Madrid ta dauka a bana, Kylian Mbapppe ya buga wasanni biyu a La Liga ba tare da cin kwallo ba, matakin da wasu suke ganin kamar akwai alamun damuwa kasancewarsa sananne wajen zura kwallaye a raga a kungiyar da ya baro ta PSG.
- Mbappe Zai Sa Riga Mai Lamba 9 A Sabuwar Kungiyarsa
- Ko Zuwan Mbappe Zai Dusashe Tauraruwar Bellingham A Real Madrid?
Mbappe ya fara karawa a babbar gasar Sifaniya ranar Lahadi 18 ga watan Agusta a gidan Real Mallorca, inda suka tashi 1-1, sannan a ranar Lahadi 25 ga watan Agusta, Real Madrid ta fara wasan farko a bana a Santiago Bernabeu, amma na biyu a La Liga a bana kuma Real Madrid din ta doke Real Balladolid da ci 3-0, inda Federico Balberde da Brahim Diaz da kuma Endrick suka ci mata kwallayen.
Koda yake kafin fara La Liga ta 2024/25, Real Madrid ta lashe UEFA Super Cup, bayan da ta ci Atalanta 2-0 a Birnin Warsaw a Poland ranar 14 ga watan Agusta, kuma Kylian Mbappe ne ya ci wa Real kwallo ta biyu a wasan, bayan Federico Balberde da ya fara zura ta farko da ya bai wa Real Madrid damar lashe kofin farko a kakar nan.
Mbappe ya fara buga La Liga a Bernabeu a karon farkko ranar Lahadi, koda yake an sauya shi da Endrick, wanda ya ci kwallo ta uku a karawar, sannan bayan tashi daga wasan Mbappe ya ce ya ji dadin wasan ya kuma yaba ga magoya baya, yadda suke karfafaawa kungiyar gwiwa.
Ya kuma ce abin farin ciki sun samu maki uku a wasan, sannan za su daura dammarar lashe sauran karawar da take gabansu tare da ganin sun yi iya yin su wajen ganin sun lashe gasar Laliga da gasar cin kofin Zakarun Turai.
Mbappe ya koma Real Madrid kan fara kakar bana, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St Germain a karshen kakar da ta wuce sai dai wasu na cewa kyaftin din tawagar Faransan mai kofin duniya ya koma Real Madrid ne, domin kwadayin lashe Champions League da kyautar Ballon d’Or.