Yawaitar Fyade A Manyan Makarantu: Tsokacin Masana Kan Lamarin

Fyade

Daga Khalid Idris Doya,

A shekarar da ta gabata ne Majalisar Dattawan Nijeriya ta gabatar da wani kuduri mai zafin gaske da zimmar dakile yawaitar cin zarafin mata da yi musu fade a manyan makaratundun fadin kasar nan.

Sai dai kuma duk da wannan kudurin, har zuwa yanzu ana cigaba da samun rahotonnin yin fyade ga dalibai gami da tursasa musu a manyan makarantun kasar nan.

A makon jiya, Kwalejin kimiyya, fasaha da kere-kere mallakin gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic) da ke Bauchi, ta kama tare da zartar da hukuncin kora ga wasu malamai biyu masu suna Adebaye Michael Sunday da kuma Abubakar Musa Baba bisa samun su da aikata babban laifi na yi wa daliban kwalejin fyade gami da lalata da su.

Ita dai kudurin dokar da aka yi kan fyade da cin zarafin dalibai da aka yi da zimmar dakile yawaitar cin zarafin mata ta nau’o’i daban-daban walau ko ta tursasa musu don basu maki ko wasu hanyoyin a manyan makarantun da suke kasar nan, dokar wacce ta ke zuwa a lokacin da korafe-korafe kan yin lalata da daliban manyan makarantu ke kara ta’azzara.

A dokar da majalisar ta gabatar, an ware wa’adin shekara 14 ga dukkanin malamin da aka cafke yana lalata da wata daliba a fadin kasar nan ba tare da wani zabi na biyu da ya wuce zaman gidan kaso na shekaru 14 ba.

Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Obie-Omo Agege shi ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, da zimmar kudurin idan ya zama doka zai kawo karshen cin zarafin mata.

A kesa-kesan baya-bayan nan da aka tabbatar tare da zartar da hukuncin kora da sallama ga wadanda aka kama da laifin a kwalejin kimiyya na gwamnatin tarayya da ke Bauchi ya tada hankalin iyaye ganin cewa suna da amincin cewa dalibansu na neman ilimi ba tare da tsangwama ba amma sai suka ji batun har yanzu dai zancen fyade na sake samun gindin zama a manyan makarantun.

A bisa wannan matakin, jaridar LEADERSHIP Hausa ya zanta da wasu masu ruwa da tsaki a fannin domin jin ra’ayoyinsu tare da ganin an dauki matakan da suka dace na kariyan hakan a gaba.

Dakta Adamu Ahmad, malami a tsangayar koyar da ilimin sanin halayyai danadam (Sociology) a jami’ar jihar Gombe, ya bayyana wa LEADERSHIP HAUSA cewar babbar matsala ne da ke ruguza yarda a tsakanin malami da dalibi kulla mummunar alaka a tsakani, yana mai cewa dukkanin fannonin na daliba da malamai ana iya samun mai laifi a ciki.

Ya kuma ce, tilasta wa dalibai amincewa da mummunar harkalla da wasu malamai ke yi shine babbar matsalar da ya dace a dakile, yana mai nusar da cewa dalibai ma suna wuce gona da iri sakamakon kwadayin neman maki ko wata alfarmar daga wajen malamai wanda hakan a karshe ke zama abun kaito.

A cewar Dakta Adamu: “Ina ganin kamar tilasta wa dalibai domin kulla wata alaka da mutane shi ne za a fi maida hankali a kai ba mu’amalar kai tsaye ba. Abun da nake nufi a bayyana ne yake, don yawanci ba za a ce wai ana kulla irin wannan mu’amala ba tare yardar su malamai da daliban nasu ba. Mafi yawa da yardarsu. Sai dai yawanci a kan tilastawa daliban ya zama sun yarda ko sun yi din, akasari suna amincewa da mummunar alakakar ce ba wai don suna son yi din ba. Saboda ko don wasu sharuddan da kila malaman ka iya gindaya musu cewa idan ba su yarda ba, ba za su ci jarabawar su ba ko in ba su yarda ba, ba za su yi kaza ko samun kaza ba.

“Sannan ana iya samun masu yi musu fyaden da nau’in fyade din (wanda shine abun kaito kai tsaye) amma a mafi yawan lokuta kamar yadda na fada maka a baya sharuddan da ake sanya musu da har zai kaisu ga amincewa da hakan ne ya fi yawa kuma a nan ne inda matsalar take.

“Wannan kenan, sannan idan za mu kalla kuma za mu ce su kansu daliban ma wani lokacin suna da matsaloli irin nasu domin za ka ga daliban ba su tsayawa inda ya kamata a ce sun tsaya. Wasu idan ba su da kokari za ka ga suna ta matsawa kusa da malamai suna kulla wani irin alaka da makamansu fiye da alakar da ta kamata a ce sun kulla a tsakaninsu da makamansu, sannan kuma wasu daliban da kansu suna neman malamai suna zuwa wajensu suna kuma tallar kawukansu domin su samu gurbin shiga don kulla alaka da malaman.”

Ya ci gaba da cewa: “Idan kuma muka kalli lamarin a shari’ance kafin a yi wannan doka da ake ta kokarin fara amfani da shi za mu iya cewa wadanda suke da ra’ayin cewa kulla alaka a tsakanin malami da dalibarsa, idan ta kai shekara 18 da haihuwa ita ma za a iya cewa za ta iya kulla alaka da kowa a waje za ta iya kuma kulla alaka da Malami a cikin makaranta (ba tilaswa, bisa amincewarta) don saboda za a iya cewa kowannensu babba ne yana da hankali.”

Shi ma dai Ibrahim M. Baba, Malamin jami’a ne a jami’ar Sojoji da ke Biu, wato Nigerian Army Unibersity Biu, da ke Jihar Borno, ya bayyana wa LEADERSHIP HAUSA cewa, illar yi wa dalibai fyade a makarantu  matsala ce babba kuma kusan wannan al’amari yanzu ya zama ruwan dare musamman a makarantunmu na gaba da sakandire, wato ‘Tertiary Institutions’.

Ya ke cewa: “Kuma kamar yadda ka sani, shi al’amari na fyade ya kan faru ne a sakamakon wasu dabi’u daga su kansu daliban da kuma Malaman. Misali, idan yarinya ta kasance mai yawaita yin shigar batsa, wato sanya tufafi wanda ke nuna tsaraicin ta a fili, to babu shakka hakan zai karkato da hankalin duk wani malami wanda zuciyarsa take da datti irin na sha’awar yin fasikanci.

“Ba fa wai sai mace ta yi shigar da ta bude fatar jikin ta ko wasu sassan jiki na tsaraici ne kawai za ta iya jan hankalin namiji ba. Ya kamata mutane su gane cewa ita mace, hatta tafin hannun ta, gashin kanta, ko kuma kafarta za su iya jawo hankalin namiji, musamman wanda dama zuciyar sa na halarce da son aikata hakan. Sanya kaya da ya matse sosai, ta yadda duk wasu surorin da za su iya daukar hankalin namiji za su bayyana a fili, shi ma babban abu ne dake iya janyo wannan matsala. Mu ma malamai ai mutane ne, kuma duk abin da kake ji a jikin ka, mu ma mukan ji.”

Ita ma Hajiya Hauwa Hussain, uwa kuma malamar makaranta a jihar Kano, sannan, shugabar gidauniyar nan mai fadi tashin kare ‘yancin mata da yara da kuma yaki da cin zarafinsu mai suna ‘Fighting Against Woman And Child Biolations’ sannan mamba ce a kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Right Network da ke karkashi HRC, ta bayyana wa wakilinmu cewa wannan matsalar na neman tashi tsaye domin tsarkake makarantu daga irin wannan mummunar dabi’ar.

“Babbar matsalatr fyade a manyan makarantu hakika kam a nawa hangen malamai su ne silar wannan abun domin su ke amfani da salon jan ra’ayi da barazana ga dalibansu da har za su kai ga cimma wata manufarsu a kan daliban. Idan kuma ana son shawo kan wannan matsalar dole sai an rufe ido an zartar da hukuncin babu sani ko sabo kan duk malamin da aka samu da aikata wannan mummunar dabi’a.

“A duk lokacin da aka samu kes makamancin wannan a tashi tsaye a yi hukunci bisa gaskiya da adalci kuma a yi wa kowa gaskiya. Shi ya sa nake jinjina wa kwlaejin kimiyya na gwamnatin tarayya da ke Bauchi bisa daukan matakin korar malamai biyu bisa samunsu da irin wannan laifin a kwanakin baya.”

Malama Hauwa ta kuma ce su kansu daliban ma suna da nasu laifin domin sukan yi shiga a wasu lokutan da ke janyo ra’ayin malaman zuwa garesu, sa ta daura wannan laifin a kan daliban da iyayensu, “Domin idan bera da sata to daddawa ma kuwa tana da wari. Saboda su kansu daliban sukan yi shiga na banza, idan malamai sun matsanta musu a ce ai manyan makarantu suke suna da ‘yancin yin yadda suke so, to dole sai an tsawatar an daina barin dalibai suna shigan da ke janyo hankalin malaman zuwa garesu.

Wata dalibar jami’ar ABU da ta nemi mu sakayk sunanta don wasu dalilai, da take matakin karatu na dari biyu a jami’ar ta bayyana cewar suna cikin tsaka mai yuwa a duk lokacin da suka ga wani malami na neman wata alaka ta hadasu, “Gaskiya ko ni wani malami ya yi kokarin jan ra’ayina kan wani badala, duk da na yi kokarin fin karfin zuciyata, sai Allah ya taimakeni a kai na samu waraka a sakamakon wasu matakai da na dauka cikin hikima da suka hada da daure wa malamin fuska a duk lokacin da yake magana da ni, sai bai samu fuskar da zai sake nemata da wani abu marar kyau ba.

 

Exit mobile version