Munanan hadurran mota da suka auku a lokacin bukukuwan da suka gabata wani abu ne mai tayar da hankala da ya kamata hukumomin da da lamuran suka shafa su gaggauta daukar matakin kawo karshen sake aukuwar su.
Ko a makon jiya ‘yansanda a Jiha Imo sun sanar da mutuwar wasu iyalai mutum 8 da hadarin mota ya rutsa da su a shataletalen Amanwozuzu da ke karamar hukumar Ikeduru ta Jihar Imo.
- NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”
- Ba Wanda Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
A kwanaki ma, matafiya 9 sun mutu a Jihar Osun a yayin da wata babbar mota ta saki hanya ta afka wa mutane, hakanan kuma a Jihar Kaduna wasu mutane 4 sun mutu yayin da mutum 56 suka jikkata a wani mummunan hadarin.
Wadannan na daga cikin hadurra kalilan da suka faru na lokacin bukukuwan da suka gabata a watan Disamba, 2023.
A rahoto na baya-bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar ya nuna, ‘yan Nijeriya 24 ke mu-tuwa a kullum sakamakon hatsarin mota.
Lamarin kuma yana kara munana ne a lokutan bukukuwa kamar kirismeti da bikin murnar sabuwar she-kara a yayin da mutane da dama suke tafiye-tafiye.
A wani rahoton kuma da Hukumar Kiyaye Hadurran Kan Titi (FRSC) ta fitar a watan Agusta na shekarar 2023, ta bayyana cewa a tsakanin watan da aka bayar da rahoton, ‘yan Nijeriya 24 su ke rika mutuwa a kullum a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuni na shekarar 2023.
Jimillar mutanen da suka rasa rayukansu a cikin wata 6 na shekarar 2023, kamar yadda FRSC ta ruwaito sun kai mutum 4,387, wanda hakan ke nuna da cewa, mutum ne 731 suka mutu, mutum 24 kenan a kullum.
Kafin wannan rahoto na watan Agusta, Hukumar FRSC ta bayyana cewa a watan Afrilu mutum 1,349 suka mutu sakamakon hadarin mota a tsakanin 1 ga watan Janairu, 2023 zuwa ranar 12 ga watan Afrilu na 2023.
Rahoton na watan Afrilu ya kuma bayyana cewa, a tsakanin lokacin da ake magana an yi hadari 2,463, ta kuma kara bayyana cewa, motoci 3,965 masu dauke da mutum 16,102 suka yi hadarin a lokuta daban-daban inda a cikinsu mutum 1,349 suka rasa rayukansu yayin da mutum 7,744 suka ji raunuka daban-daban.
Jami’in wayar da kan al’umma na hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya lura da cewa, hadurran sun auku ne a jihohi 36 na tarayyar Nijeriya da kuma yankin babban birnin tarayyar Abuja, ya kuma ce, “Daga Janairu zuwa Yuni, mutum 4,387 sauka mutu sakamakon hadurran mota yayin da kuma mutum 14,108 suka ji raunuka daban-daban.”
Abin takaici shi ne yadda ake asarar rayukan al’umma a kullum, ba a dauki rayuwa da muhimmanci ba a Nijeriya, ana kashe mutane ta hanyar gangaci amma babu wanda ake kamawa da laifin wannan ta’asar.
Amma kuma hadurran motoci sun fi yawaita a lokutan bukukuwa saboda yadda mutane ke tururuwan ganin sun koma garuruwansu na asali don gudanar da bukukuwan, abin har ya zama jiki.
Duk da mastalar tsaro da ake fuskanta a sassan Nijeriya, al’umma sun gwammace su yi tafiya ta hanyoyionmu musamman ganin yadda kudaden sufurin jirgin sama ya yi tashin gwauron zabo, ta yadda ya fi karfin talakan Nijeriya.
Amma kuma wasu da dama na tsoron tafiya ta hanyoyinmu saboda yawaitar hatsurran da ake samu wanda kuma yakan ya fi tsanani a lokutan bukukuwa.
A matsayinmu na gidan jarida muna sane da dalilan da ke kara yawaitar hadurran a manyan hanyoyin kasar nan, wadanda suka hada da ko dai halin da hanyoyin ke ciki da kuma halin da motocin ke ciki ko kuma gangaci daga masu tukin.
Duk da cewa, wasu dalilan na taimakawa wajen afkuwar hadurra a hanyoyinmu amma matsalar rashin kyawun hanyoyinmu ne a kan gaba wajen haifar da hatsurra a kasar nan.
In ka duba Gabas, Arewa, kudu da yammancin kasar duk lamarin daya ne, hanyoyin sun lalace. Hanyoyin Nijeriya sun yi lalacewar da a wasu wuraren manyan ramuka masu zurfi ne suka mamaye su gaba daya.
Rashin ingancin motocin da ake amfani da su shi ma babbar matsala ne da ya kamata a kawo wa dauki. In an sa ido yadda ya kamata za a iya rage motocin da ba su da lafiyar da ta kamata a hau hanya don yin tafiye-tafiye da su.
Sa ido don gano motocin da suke da matsala da kuma tsaurara hanyoyin karbar lasisi na da muhim-manci. Haka kuma ya kamata a kara horas da jami’an kula da motoci tare da ba su karfin kawar da mo-tocin da suka karya doka daga hanyoyinmu.
Haka kuma dole direbobi su kula yayin da suke a kan hanya don kauce wa aukuwar hadari, su bi duk-kan dokokin hanya tare da mutunta sauran masu amfani da hanyar.
Akwai bukatar jami’an FRSC da jami’an ‘yansanda su tabbatar da hukunta masu karya dokokin hanya, kamar masu gudun wuce kima da wuce moto ba bi sa ka’ida ba.
A kan haka, wannan jaridar ke kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su dauki matakan kariya daga af-kuwar hadari a kan hanyoyinmu da matukar muhimmanci.
Ya kamata gwamnati ta jagoranci kawo karshen mace-mace da raunukan da ake ji a hanyoyinmu, lokaci ya yi da za a dauki kwakkwaran mataki, ‘yan Nijeriya sun cancanci samun hanyoyi ba tare da fargabar hadari ba a lokutan bukukuwa.