Connect with us

ADON GARI

Yawan Ba-ni-ba-ni Na Rage Daraja Da Kimar Mace A Wurin Miji – Hajiya Zainab

Published

on

Idan Mutum Ya Zauna Da Kowa Lafiya, Zai Samu Kwanciyar Hankali
Abin Da Za A Yi Zaman Aure Ya Yi Dadi Sosai

A kullum burin galibin mata da suka samu ci gaba da rufin asiri na rayuwa shi ne su jawo sauran mata ‘yan’uwansu zuwa turbar da suke kai domin su ma su dandani dadin rayuwar da suke ciki. A kan haka ne, bakuwarmu ta yau ta karfafa gwiwar mata a kan muhimmancin sana’a bag are su ba kawai har da zamantakewarsu ta aure. A karanta hirar har karshe a karu da darussa masu ma’ana, kamar haka:

Barka da isowa hajiya Zainab kafin komai zamu so Jin Takaitaccen Tarihinki.

Da farko dai sunana Zainab Adam, wacce aka fi sani da Zee/Zee’s kitchen.
An haife ni a Karamar Hukumar Zariy da ke Jihar Kaduna. Na yi karatun Firamare a Tsoho Abdullahi Tukur tukur da ke Zariya, in da na yi JSS dina a Government Secondary School Tudun Jukun Zaria. Sai SSS dina a GGSS Kongo Zariya. A inda nan ne na tsaya, ina SS2 na yi aure. Ina zaune yanzu a Kaduna, kuma na ci gaba da karatun Sakandare GGSS U/Mu’azu Kaduna na gama. Na kuma gama Diploma na a Kadpoly inda na karanci Business Administration (Tafiyar da Kasuwanci). Ina da aure da yara 3, Alhamdullah, masha Allah.

Ko za mu iya jin matakin da kike a bangren aiki ko kasuwanci da sauransu a halin yanzu?

Alhamdullah masha Allah. Yanzu dai bana aiki sai dai kasuwanci ina tabawa kuma alhamdullah ina jin dadin sa.

Hajiya Zainab masu karatu za su so ki yi dan tsokaci a kan zamantakewa na rayuwa musamman a ce bangaren rayuwa irin ta aure?

Shi zamantakewa ta rayuwa gaba daya komai hakuri ne da kuma iyawa. Bare idan aka ce zamantakewar aure, wannan ko wanda bai shiga ba ma ya san dan hakuri ne. Zama ne na dibara, hadiye komai da za a yi maka face bai saba wa Allah da zaman auren ba. Tausayin juna da kula da juna, idan ka iya wannan in sha Allah zaman auren ki/ka babu matsala kuma ba za a ji kanku ba. Duk da an ce shi zaman aure zo mu zauna ne zo mu saba, dole akwai wannan. Amma hakuri ne maganin komai.

A yanayin zama na rayuwar yau da kullum akwai wani kalubale da kika taba fuskanta ko dai ta bangaren aiki ko sana’a da sauransu?

Gaskiya babu, saboda na yarda da cewa in ka zauna da kowa lafiya toh kai ma in sha Allah za ka samu kwanciyar hankali. In ba ka yi cuta ba, babu mai cutar ka da yardar Allah. So, alhamdullah babu.

Wace gudunmawa kike da ita da za ki iya bawa al’umma Wanda za su amfana?

Gudummawar da zan bawa al’umma ita ce shawara ce ga al’umma gaba daya, mata da maza, a tashi a nemi na kai, a kama sana’ar hannu domin dogaro da kai. Aikin gwammnati na da kyau amma yana da kyau ka san sana’ar hannu ka kuma iya shi. Kana na gwamnati kana na hannun wata ya yi nisa ba a biya ba, ba ka da fargaban abin da za ka ci da iyalan ka. Ko miji bai yi ba, ke mace daure ki yi, domin ki tallafa masa

Wacce shawara za ki bawa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum wadda idan suka yi koyi ko amfani da ita rayuwa za ta inganta?

Shawara ta wajen al’umma ita ce komai za ka yi ka sanya tsoron Allah, ka da ka ci amana a kuma rike Allah da fadar Manzonsa (SAW). A taimaka wa juna, a yi duba zuwa ga na kasa da kai domin a taimaka masa daga cikin abin da Allah ya hore maka.
Idan ka yi wannan, in sha Allah za ka yi rayuwa mai inganci.

Kamar yanzu na san wajen da na tambayi aiki kin ce kina kasuwanci, to Hajiya Zainab shin ko za ki iya fada mana abin da ya ja ra’ayinki har kika fara sana’a?

Eh toh, ni gaskiya tun ina karama ina son sana’a domin gidan mu gidan sana’a ce. Ina ganin iyayena na yi, kafin mahaifina ya ce gashi sun fitar da nasu sun yi amfani da shi. Hakan da suke yi yana burge ni yana kuma rufa mana asiri. Tun ina gida ina taba sana’a abina, yanzu ma da na yi aure, na ga zaman ba zai yi min ba, yawan ba-ni-ba-ni wajen miji rage kima take da daraja da takura, sai duk ka ishi miji ka gundure shi, shi ma akwai abubuwa a gabansa, dole ki taimaka masa, duk da za a yi maka amma fa ba komai ba. Shi ya sa na fara sana’ata daga kadan-kadan, in na yi wannan na kama wannan wanda Alhamdullah, Allah ya sa min albarka a ciki kuma muna samun albarkar iyaye komai na tafiya da kyau.

Masha Allah Hajiya Zainab ko za mu iya jin irin kasuwacin da kike, sannan ya kike ganin wannan sana’a taki za ta taimaka ma al’umma?

Toh Alhamdullah, ina taba kasuwanci na kayan kitchen, hijabai, materials da kuma abin da ba za a rasa ba. Toh, tana taimakawa al’umma domin kayan namu ba mu daura masu kudi da yawa ga mai sari ko sayen daya, ta nan masu saye na samun sauki, wanda suka sami ragi su yi wata hidimar gaban su da shi.

Toh Hajiya Zainab yanzu misali a ce mutum yana so ya fara irin wannan sana’a taki ta sayar da kayan kitchen da kuma hijabai da materials, ta yaya kike ganin zai fara ko kuwa ta yaya ya kamata ya fara?

Duk Wanda yake da bukatar fara wannan kasuwanci zai iya tuntuba ta, ina badawa a kan sari kamar yadda za ka saya a kasuwa.

Shin akwai wani alheri da ke tattare da wannan sana’a da za ki bayyana wa masu karatu?

Alhamdullah akwai alkhairi. Domin alkhairin da ke cikin sa ya sa muke ciki har yanzu.

Ko za ki iya fada wa masu karatu sirrin da ke cikin wannan sana’a?

Sirrin da ke cikin sa shi ne iya mu’ala da abokan hulda masu sayen kaya (customers), rikon amana da fadar gaskiya da kuma bin riba kadan ka nemi albarkan da ke cikin sa.

Kina ganin akwai hanyar da Gwamnatin za ta iya shigowa cikin wannan sana’a taku?

Toh, idan Gwamnati na son taimaka mana, muna maraba da ita, domin kuwa irin mu masu neman nakai a duba masu karamin jari ta kara tallafa masu domin su ma su tallafa wa wadanda ke son shigowa ciki. Akwai wadanda suke kula da sha’anin koyar da sana’o’i, a sa su suna nemo irin mu lungu da sako ana tallafa mana, ta nan mun san eh Alhamdullah Gwamnati na farin ciki da wannan kasuwanci namu sosai.

Me za ki ce wa LEADERSHIP A Yau Juma’a?

Tabbas kam LEADERSHIP A Yau Juma’a jarida mai albarka, wadda ke fito da kukan jama’a har ta kai ga duniya sun san halin da wani ke ciki, har a kawo masa tallafi ko dauki. Ina maku fatan alkhairi da kira gare ku ku ci gaba da abin da kuke yi, aikin alkhairi yana da lada. Allah ya taimaka maku, ya kara maku daukaka, amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: