Alkaluman da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar a yau Jumma’a, sun tabbatar da cewa, a watan Nuwamban shekarar da muke ciki, yawan jarin waje da kasar ta yi amfani da shi ya karu da kaso 26.1 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kana, daga watan Janairu zuwa Nuwamba, jimillar jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi ta kai kudin kasar Yuan biliyan 693.18, adadin da ya ragu da kaso 7.5 bisa dari, kuma yawan raguwarsa ya ragu da kaso 2.8 bisa dari, bisa na watanni 10 na farkon bana. Wato yawan raguwar jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi ya sauka.
Kazalika, adadin sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar Sin, ya ci gaba da karuwa cikin sauri, inda ya kai 61,207 daga watan Janairu zuwa na Nuwamba, adadin da ya karu da kaso 16.9 bisa dari. Kana, a watan Nuwamban dai, adadin sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar Sin ya kai 7,425, wanda ya karu da 35.3 bisa dari. (Murtala Zhang)














