Kungiyar jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kudin jigilar kayayyaki na kasar na shekarar 2023, wanda ya kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 352.4, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 49, karuwar kashi 5.2 cikin dari bisa makamancin lokacin shekarar 2022.
Yawan kudin jigilar kayayyakin amfanin gona na kasar na shekarar 2023 ya kai Yuan triliyan 5.3, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 737.2, wanda ya karu da kashi 4.1 cikin dari, yayin da yawan kudin jigilar kayayyakin masana’antu ya kai Yuan triliyan 312.6, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 43.5, wanda ya karu da kashi 4.6 cikin dari kan na shekarar 2022. (Zainab Zhang)