Yawan Kudin Kayayyakin Da Aka Shigo Da Su Daga Kasashen Waje Zuwa Sin Da Aka Saya Ta Yanar Gizo Ya Zarce Yuan Biliyan 100

Daga CRI Hausa

Alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, yawan kudin kayayyakin shigi da fici wadanda aka saya ta yanar gizo a shekarar 2020 ya kai Yuan triliyan 1.69, karuwar kashi 31.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Sayayya ta yanar gizo a tsakanin kasa da kasa ta kasance sabuwar hanyar bunkasa cinikin waje na kasar Sin.

A watan Mayu na bana, an gudanar da bikin cinikayya ta yanar gizo a tsakanin kasa da kasa karo na farko a birnin Fuzhou dake kasar Sin, inda kamfanoni 2363 suka halarta, wadanda suka shafi dandalolin sayar da kayayyaki ta yanar gizo guda 33 a duniya. (Zainab)

Exit mobile version