Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa yawan ma’aikata a ƙananan hukumomi ne ya hana gwamnati fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.
A cewar gwamnan, Jihar Borno na da ma’aikata sama da dubu 90 a ƙananan hukumomi 27, yayin da Jihar Kano ke da ma’aikata dubu 30 kawai a ƙananan hukumomi 44.
- Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
- Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Kwaskwarimar Majalisar Dokoki Kan Naira Biliyan 7
Wannan ne ya kawo cikas wajen aiwatar da sabon tsarin albashi.
Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomi da su tsara yadda za su iya biyan albashin cikin tsari mai ɗorewa.
Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Ƙananan Hukumomi da Masana’antu, Modu Alhaji, ya ce a wasu lokuta Gwamnatin Tarayya na turo ƙasa da Naira miliyan 700 zuwa asusun ƙananan hukumomi, alhali ana buƙatar kusan Naira miliyan 778 don biyan albashi.
Gwamnatin Borno na ci gaba da ƙoƙarin ganin ta samo mafita domin iya biyan sabon albashin ma’aikata kamar yadda aka tsara a matakin ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp