Shugaban hukumar kididdiga ta kasa (NPC), Hon Nasir Isa Kwara, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da sauran kasashen duniya kudurin gwamnati na samar da sahihin bayanan yawan al’ummar Nijeriya da aka kiyasta a halin yanzu sun kai miliyan 223.
Hon Kwara ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da ministar harkokin jin kai, Dakta Betta Edu, wadda ta bayyana muhimmancin sanin bayanan da za su taimaka wajen isar da ajandar wannan gwamnati.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Fatali Da Zargin Da Obi Ya Yi Mata Kan Karin Kasafin Kuɗi
- Yawaitar Mutuwar Farad-daya A Nijeriya
Shugaban NPC ya yi alkawarin bai wa ma’aikatar cikakken bayanan daga kidayar jama’a da gidaje da za a gudanar nan gaba kadan. Ya bayyana cewa hukumarsa ta gano gidaje miliyan 65 a yayin gudanar da kidayar gwaji da aka yi a fadin kasar nan.
A cewarsa, hukumar ta kuma gano wasu mutane na musamman da ba sa zama a gidajen da aka saba, wadanda suka hada da ‘yan gudun hijira, masunta, makiyaya da kuma wadanda ke zaune a karkashin gadoji da dai sauransu.
Ya ce tuni hukumar ta kammala siyan kayayyakin da suka dace domin yin kidayar jama’a da gidaje masu zuwa. Ya kara da cewa hukumar ta kebe kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan kuma tana da taswirorin wuraren zama, ofisoshi, tasoshin ruwa da sauransu.
A nata jawabin, minintar jin kai, Dakta Edu ta kalubalanci shugabannin NPC na bukatar da akwai na samar da sahihin bayanan yawan ‘yan Nijeriya da zai taimaka wajen gudanar da shiryae-shiryen ci gaban kasa da za a kaddamar.
Dakta Edu ya ce, “A nan muna tare da shugaban hukumar NPC da tawagarsa daga hukumar kidaya ta kasa a ma’aikatar jin kai na neman hadin gwiwa da ma’aikatar.
Su ne masu kula da bayanan da muke da su a Nijeriya, bayanan kidayar jama’a da sauran muhimman bayanai masu muhimmanci za su taimaka mana wajen cimma ajandar gwamnatin Shugaba Tinubu.