Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce mafi yawan ‘yan siyasar Nijeriya ba su da tarbiyya tun daga Æ™uruciyarsu, shi ya sa suke aikata cin hanci da rashawa.
Sanusi ya faÉ—i hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a daren ranar Laraba.
- Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bayar Da Kiwon Lafiya Kyauta Ga ‘Yan Fansho Masu Karamin KarfiÂ
Ya ce mutane da dama da ke riƙe da muƙamai a gwamnati, ba a koya musu gaskiya da riƙon amana ba tun suna yara.
“Yawancinsu sun shiga gwamnati ne saboda dalilai marasa kyau. Ba su da tarbiyyar shugabanci,” in ji shi.
Sanusi ya ce: “An rusa É—abi’u da tarbiyyar kirki a Æ™asar nan. Mutanen da ke mulki yanzu ba su da tarbiyya kuma ba su da wani abu na Æ™warai da za su bari a baya.”
“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin É“arayi ba.”
Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu.
“Yawancin shugabanninmu sun shiga ruÉ—ani, babu wanda ya tsira,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp