A ko da yaushe zabe a Nijeriya ya kan kasance ne bisa la’akari da kuri’un da ake jefawa a yankuna.
Wannan lamari ne da ke turnike zaben kasar nan tun a shekarar 1959 lokacin da yankin arewa ya fi samun kujeru masu yawa da aka amince na yin sulhu wajen hawa karagar mulki.
- Kashi 31 Na ‘Yan Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Rubutu Ba ― Gwamnatin Tarayya
- Kwastam Ta Damke Mazakutar Jaki 7000 Da Miyagun Kwayoyi A Legas
Tun bayan da kawo mulkin dimokuradiyya, yankin arewa yana taka muhimmin rawa a cikin harkokin dimokuradiyyar kasar nan.
Mafi yawancin shugabannin da suka lashe zabe dole ne sai sun samu nasara a yankin arewa maso yammacin Nijeriya, duk da ba shi ne samun nasara na karshe a zabe ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dade yana samun nasara a yankin arewa maso yamma, tun a shekarar 2003 mafi yawancin abokan karawarsa suna faduwa zabe a wannan yankin.
Yankin arewa maso yamma ta hada wasu jihohin da suke da harafin K har guda hudu, Kano, Kaduna, Katsina da Kebbi, wanda suke iya samar wa dan takara sama da kuri’u miliyan uku, wannan ya danganta ne da yanayin dan takarar.
Mafi yawancin ‘yan takara suna lashe zabe ne a tsakanin kuri’u miliyan 15 zuwa 17, sai dai Jonathan da ya samu kuri’u miliyan 20, wanda ba a taba samu ba tun bayan shekaru 10 da suka gabata.
Yankin arewa maso yamma ya kasance yankin da ake bai wa ‘yan takara dauki, sai dai kabalanci da addini suna taka muhimmiyar rawa a yankin.
Ba za a taba musanta cewa ‘yan Nijeriya suna amfani da kabila da addini wajen zaben dan takara ba.
Sai dai abin da yafi dacewa shi ne, samun kasa daya ba tare da la’akari da yanki ko addini ba.
Abun tambaya a nan shi ne, ina kuri’an yankin arewa maso yamma za su kasance? Wasu na ganin cewa Tinunbu yana da tabbacin lashe wannan yankin, amma tambayan ita ce, ta ina zai iya samun nasarar? Wannan lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.
Wasu na ganin cewa an samu sauyin jefa kuri’a a yankin arewa maso yamma sakamakon irin kiraye-kirayen da malaman addini ke yi.
Haka kuma wasu ‘yan siyasa a yankin arewa sun dage a kan sai mulki ya dawo arewa ta hannun Atiku, inda suka tabbatar da cewa kuri’un yankin arewa maso yamma za su kasance na Atiku ne.
Wasu kuma na ganin Peter Obi da Kwankwaso na iya taka rawa a wannan yankin. Bayan addni da kala da suke da tasiri a yankin arewa maso yamma, kudade ma za su taka muhimmiyar rawa a yankin.
Wasu na ganin cewa wannan ita ce siyasa mafi tsada da za a gudanar a kasar nan.
A yanzu da ya rage saura kasa da kwani 170 a gudanar da zabe, abu guda daya shi ne, duk wanda ya lashe yankin arewa maso yamma shi zai ci nasara a zabe? Lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.
A yawan masu rajista da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar, yankin arewa maso yamma shi ke kan gaba, inda yake da yawan masu jefa kuri’a guda 22,672,373.
Wannan bayani yana cikin shafin hukumar INEC, inda ta nuna cewa ta samu karin masu rajistar zabe guda 12,298,932 a zaben 2023.
Gaba daya jimillar jihohin arewa masu yamma sun hada da Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Sakkwato da kuma Zamfara, da suke da yawan masu jefa kuri’a guda 22,672,373 a zaben 2023.