An Yi Wa Jam’iyyar NRM Kyakkyawar Tarba A Karamar Hukumar Gusau

A ranar Asabar din da ta gabata ne Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa ‘NRM’ (National Rescue Mobement) ta gudanar da taro a Babban Ofishinta na Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Taron ya samu amsuwa da tarba ta musamman daga al’ummar karamar Hukumar Gusau, wadanda suka hada mata da maza; manya da matasa.

Shugaban taron, Alhaji Sa’adu Mai Yadi Gusau ya bayyana cewa, “al’ummar Karamar Hukumar Gusau, mazansu, mata da matasa sun kwashe komi nasu daga jam’iyyun APC, da PDP, da sauran jam’iyyu zuwa wannan jam’iyyar ta NRM, mai ceton al’ummar kasa. Kuma mun aminta da jam’iyyar ne sakamakon ganin Sanata Sa’idu Dansadau a cikinta dumu-dumu, saboda mun aminta da shi, don haka muka tabbatar babu batun cuta a ciki, sai dai ceton al’umma.

“Kuma al’ummar jihar Zamfara mun tabbata cewa babu wanda ke san ci gaban talakan kauye da birni sama da Sanata Dansadau, domin shi ne wanda yayi zarra ya fito fili ya bayyana wa duniya halin da jihar Zamfara ke ciki na mawuyacin halin kisa da kona dukiyoyi. Wanda shi ne sanadiyyar kawo rawar daji da kuma zuwan shugaban kasa a dajin Dansadau. Don haka mu al’ummar karamar hukumar Gusau mun amshi wannan jam’iyyar hannu biyu tsakaninmu da Allah, don ita ce, za ta ceto al’umma daga bakin zaluncin da muke ciki.” inji shi

Shi ma Muhammad Sarkin makera, ya bayyana cewa, sun wasa kuri’arsu don sarar azzalumai a ranar zabe. “Don haka babu ko shakka Sanata Dansadau, Zamfara taka ce, kai ka san haka, baka da matsala. Tuni dubban matasa da mata ke jiraye da kai don amsar wannan jam’iyyar hannu biyu, mai ceton al’ummar kasa.

Baban bako a taron shi ne, Shugaban Jam’iyyar NRM na Kasa, Sanata Saidu Dansadau. A jawabinsa ya bayyana cewa, bai yi mamakin ganin wannan taron ba don ya san al’ummar Jihar Zamfara sun gaji da wannan mayaudariyar gwamantin ta APC, wacce ba ta dauki rayukan al’umma da muhimmanci ba. “Domin ran dabba ya fi na dan Adam daraja a kasar nan, kuma gwamnatin kasar nan ta jefa al’umma cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa. Mahukuntan kasar sun fifita kansu akan kowa, asibtitocinsu daban, makarantunsu daban, komai nasu daban.

“Cikin sharuddan jam’iyyar NRM, babu wani mai mukami a cikin gwamanti da zai kai dansa makarantun kudi, sai ta gwamnati. Haka ma asibitoci shi ma sai na gwamnati. Don haka babu wani bambanci da fifita wani a lokacin da jam’iyyar mu ke mulki kowa za mu dauke sa bai daya babu bambanci.”

Sanata Dansadau ya kara da cewa; “Kuma wannan tambarin na Zuma, ga Zaki ga magani don za ta magance matsalolin al’ummar kasar nan da  yardar Allah. Kuma ba za ta bar azzalumi ba ya na yawo sai ta harbeshi, a duk inda ya ke.”

Shi ma Shugaba na Jihar Zamfara, Alhaji Danbuba Muhammad ya bayyana cewa, wannan jam’iyyar, jam’iyya ce ta sadaukarwa don mu girbi alherin da ke ciki. Don haka kowa ya zo mu kama hannu mu ture wannan azzalumar gwamnatin dake shan jinin jama’a. “Kuma wannan jam’iyyar za ta tafi da kowa da kowa, kafada da kafada don ganin ta samu nasara.

 

Exit mobile version