Kwamishina mai wakiltar jihar Kaduna a Hukumar ƙidaya ta ƙasa, Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi ta kawo ziyara jihar Kaduna domin ganawa da shugabannin Ƙananan Hukumomin jihar 23, tare da masu ruwa da tsaki, a shirin Hukumar na wayar da kan jama’a game da ƙidayar da ke tafe.
A lokacin da ta ziyarci Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Hajiya Sa’adatu ta bayar da shawara ga al’umma kan cewa su fito ƙwan su da ƙarƙwata, su tabbatar da an ƙidaya su, domin ta haka ne kawai gwamnti za ta iya wadatar da su da ababen more rayuwa.
- Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya
- Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan
Haka kuma Kwamishiyar ta jawo hankalin jama’a game da mahimmacin yin rajisista don karbar shaidar yin aure, haihuwa, saki, mutuwa da dai sauran su, wanda ake bayarwa a ofishin Hukumar a duk jihohin ƙasar nan.
Hajiya Sa’ah ta kuma bayyana cewa ita wannan ƙidaya da yin rajistar haihuwa, aure da sauran su, abubuwa ne masu muhimmanci da za su taimaka wa gwamnati ta san yawan su, ta yadda za su sami nasarar ci gaba da lasar romon Dimokraɗiyya mai yawa, musamman a bangaren ilmi, lafiya da dai sauran abubuwan more rayuwa.
Daga nan ne ta jinjina wa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da cewar jihar Kaduna ce jiha ta farko da gwamnan ta ya yi yunƙurin gabatar da wayar da kan al’ummar sa game da muhimmancin ƙidaya, kuma lallai yana bayar da cikakken goyon bayan sa a kan haka, inda ya ɗauki nauyin hakan a dukkan Ƙananan Hukumomin jihar.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Malam Jamilu Abubakar Albani (ALGON), wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, ya bayyana cewa su a shirye suke su bayar da dukkan goyon bayan da ake nema.
Ya ce, su tun a baya sun fara wayar ma al’ummar Ƙaramar Hukumar su kai game da manufa da muhimmancin shirin ƙidayar a gare su. Sun shiga lungu da saƙo don wayar ma da al’ummar su kai game da shirin ƙidayar da ke tunkarowa, wanda zai gudana nan ba da jimawa ba.
Ɗaya daga cikin Malaman addinai da suka halarci taron ya tabbatar da ƙidayar al’umma a cikin tsarin addinin musulunci, domin shi ne yake bada damar sanin tsatson dukkan ɗan adam da kuma tabbatar da rayuwa cikin tsari.
Shi ma a nasa jawabin, wani Shugaba a addinin kirista ya nuna farin cikin sa, sannan kuma nuna yadda zasu wayar ma da mabiyan su kai game da ƙidayar. Ya kuma ƙara da ceawar a koyaushe hukumar ƙidayar suka shirya, su ma a shirye suke wajen ganin an cimma gaci.
A looacin da tawagar Kwamishiyar ta isa Ƙaramar Hukumar Soba, Shygaban Ƙaramar Hukumar, Hon. Muhammad Shehu Lawal Molash, ya bayyana jin daɗin sa da wannan shiri na ƙidaya, inda ya nuna cewa za su bayar da duk gudumawa da haɗin kan da ake nema don samun nasarar aikin.
Shi kuwa Sarki Haladu, jan hankalin matasa ya yi da su kauce ma duk wata hayaniya, su zama masu natsuwa tun a yanzu wajen wayar ma da al’umma kai har zuwa kammala shirin.
Ya zuwa haɗa wannan rahoton dai, Kwamishiniya Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi tana ci gaba da zagawa zuwa sauran Ƙananan Hukumomin jihar don ƙara wayar da kan jama’a game da muhimmancin wannan ƙidaya da ke tafe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp