Abubakar Abba" />

Yin Bacci Na Awa 9 Da Dare Zai Iya Shafar Tunanin Dan’adam – Bincike

Ma fi yawanci an sani cewar, mutane da suka yi barci kasa da awa biyar da dare, hakan zai iya shafar tunin su.

Amma sai dai, a wani bincike da aka gano ya nuna cewar,  mutanen da suka shafae awa tara suna yin barci da dare, hakan zai iya shafar tunin su.

Masu gudanar da bincike sunyi dubi akan sakamakon gwaje-gwajen tunin mutane kimanin 400,000. 

Idan aka kwatanta da mutane da suke shafe awa bakwai suna barci, amma wadanda aka ruwaito suna yin barcin awa tara, dukkan su za su iya fuskantar matsalar tunani kasa da mutanen da suke yin baccin da dare zuwa awa biyar.

Sai dai, a wannan binciken ba a yi la’kari da cewar, dan’adam mace ne ko namji ba ko kuma yin amfani da shekaru.

Bugu da kari, biciken ya kara da cewa, wadanda suka yi bacci da dare har na awa goma sun kai kashi sha daya na yin kuskure.

Har ila yau, binciken ya bayar da shawarar cewar, yin dogon bacci da dare, ai iya shafar kyakyawan tunin da ya kama dan’adama ya yi da kuma samun da mumuwa a cikin baccin .

Kwararrun kiwon lafiya sun yi ittifaki cewar, mutane da suka yi dogon bacci da dare, mai yuwa za su iya fuskantar rashin ingantaccen bacci, inda hakan zai kuma iya sanya wasu yankuna na kwakwalwara su gazawar sadar da bayanai zuwa inda suka kamata da kuma  yiwuwar cushewar kwakwalwa.

Binciken bai kuma yi amfani da ko wadanda aka yi gwajin akansu suna  fuskantar wata matsala ta rashin lafiya ba.

Dakta Bictoria Garfield, babbar jami’ar kiwon lafiya kuma wadda ta kirkiro tare da  jagoranci binciken ta sanar da cewar, kwarai yin gajeren baccin dare ga dan’adam zai iya janyo masa matsala a kiwon lafiyarsa, amma kuma yin dogon bacci da dare har na awa tara zai iya shafar kiwon lafiyar dan’adam.

A cewar Dakta Bictoria Garfield, babbar jami’ar kiwon lafiya, “ Wasu mutanen suna yin tunanin cewar,  kwanciya da dare don yin dogon bacci abu ne mai kyau, amma bincike ya nuna cewar, yin dogon bacci da dare zai iya janyowa tunin dan’adama illa.

Shi ma wani kwararren a fannin kiwon lafiya Albert Henry wanda shi ma yana daya daga cikin tawagar da suka gudanar da wannna binciken wanda aka wallafa a Mujallar International Epidemiology yace, “ Mun gano yan hujjoji yin dogo ko gajeren bacci zai iya janyo kamuwa da cutar da mai yinsa.

A karshe, Albert Henry  ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a kara zurffa yin bincike a kan wannan lamarin.

Exit mobile version