Abubakar Abba" />

Yin Noma Ta Hanyar Kimiyya Zai Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya – Rahoto

aikin Noma

Wani rahoto da sashen kudi na kamfanin (FDC) ya fitar ya bayyana cewa, in har Nijeriya ba ta yi amfani da hanyar Kimiyya wajen bunkasa aikin noma, samar da danganta tsakanin masu ruwa da tsaki da samar da damar makin zuba jari a fannin aikin noma ba, kasare ba za ta iya ciyar da tattalin arzikinta ko kuma janyo masu zuba jari a fannin aikin noma ba.

Rahoton na kamfanin FDC wanda aka saba wallafa shi duk wata, an fitar da shi ne a makon da ya gabata, inda rahoton ya ce. Idan aka bai wa fannin kulawar da yakamata, zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar da kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan.
A cewar rahoton, a karni biyu da auka wuce, fannin aikin noma a Nijeriya na samar da akalla kashi at 20 bisa dari na tattalin arzikin kasar.
Sai dai, rahoton ya koka kan kasar ta gaza wajen mayar da hankali a kan fannin mai don bunkasa tattalin arzikin kasar mai makon mayar da hankali a fannin aikin noma domin bunkasa tattalin arzikin kasar, inda rahoton ya ce, in har gwamnatin ta mayar da hankali kan kokarinta na bayar da kwarin gwiwa kan yin noma na zamani, hakan zai rage tsadar isar da bayanai zuwa ga manoma daga gun masu son zuba jari a fannin da kuma daga gun gwamnati.
Rahoton ya yi nuni da cewa, hakan zai kuma rage tsadar yin noma da kuma samun damar sayen kayan aikin na a sauki tare da kuma samar da sauki ga masu zuba jari a fannin aikin noma ta hanyar hada manoman da hukumomin da ke bayar da bashin aikin noma a kasar nan, inda kuma rahoton ya yi nuni da cewa, mayar da hankali kan yin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani zai rage bata lokaci wajen tura kudade ga fannin aikin noma.
A wata sabuwa kuwa, kungiyar manoman Tumatir ta kasa ta kara yin kira ga hukumomin da abin ya shafa dasu samar da ingantaccen Tumatir ga manoman da ke a fadin kasar domin a kara bunkasa nomansa a kasar ta kuma ta kuma kara kokawa kan karancin Irin na Tumatir da manoman sa a kasar nan su ke ci gaba da fuskanta.
Shugaban ta na kasa Sani danladi-Yadakwari ne ya sanar da hakan a hirarsa da mamema labarai, inda ya ci gaba da cewa, manoma na ci gaba da fuskantar karancin Irin Tumatir na zamani ganin cewa lokacin noman sa ya fara tunkarowa kasar nan.
danladi wanda ya bayyana haka a jihar Kano ya ci gaba da cewa, Babban Bankin Nijeriya ta ba kamfanin dangote naira biliyan 1.58 domin samar wa manoman ingantaccen Irin Tumatir na zamani daga kasashen waje, inda ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, mutane 452 ne kawai suka samu wannan iri cikin manona 10,000 da suka yi rajista da mu.
Ya ci gaba da cewa, abin da ke tada mana hankali shine idan har ace zuwa yanzu ba a iya samar wa manoma wannan iri ba, to fa lallai akwai yiwuwar ayi fama da karancin Tumatir a cikin shekara mai zuwa.
Shugaban ya kara da cewa, shi Tumatir akan noma shi ne a lokacin rani, zuwa tsakiyar watan janairun 2020 idan ba a iya samar wa manoma da dama irin ba to shike nan sai dai kuwa wata shekarar domin daga lokacin ba zai yiwu a noma Tumatir din ba.
Yadakwari ya ce yakamata ace zuwa yanzu an rabawa akalla koda rabi ne daga cikin manoman da suka yi rajista da kungiyar amma ace wai manoma dari hudi da ‘yan kai ne suka iya samun wannan iri.
Ya yi kira ga Kamfanin dangote da aka ba kwangilar shigo da wannan iri da su gaggauta samar wa manoma irin domin fa an kashe kudi wajen gyaran gona domin wannan aiki.
Da ya ke yin tsokaci kan matsalolin da aka sami wajen samar da irin shugaban Kamfanin Gonakin dangote, Abdulkarim Kaita ya bayyana cewa sun samu matsala ne da babban bankin Nijeriya CBN wajen samar musu da kudaden sannan kuma ko a wajen shigo da irin sai an dauki lokaci wajen wanyewa da jami’an hukumar shige da fice ta kasa.

Exit mobile version