• English
  • Business News
Wednesday, July 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yuan (RENMINBI) Na Ci Gaba Da Samun Farin Jini A Kasashen Afirka 

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 weeks ago
in Ra'ayi Riga
0
Yuan (RENMINBI) Na Ci Gaba Da Samun Farin Jini A Kasashen Afirka 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kasashe da dama na nahiyar Afirka sun jima da kulla dangantakar cinikayya da China, ta yadda zai kasance abu mawuyaci a samu gidan da ba a amfani da kayan da aka kera a kasar Sin. To sai dai sakamakon kakagidan da dalar Amerika ta yi a harkokin cinikayya na kasa da kasa ya sanya ake samun tarnaki a harkokin kasuwanci tsakanin wannan kasa da waccan kasa.

Tun fil azal, akwai dadaddiyar alakar cinikayya tsakanin China da Nijeriya, hasali ma dai China ita ce babbar kasa da ta fi kowace kasa huldar kasuwanci da Nijeria. Hada-hadar kasuwanci tsakanin China da Nijeriya ta kasance mai armashi, kuma mai amfanar dukkan bangarorin biyu. Bisa ga wannan dalili ne China da Nijeriya suka ga akwai bukatar rage dogaro da dalar Amerika wajen gudanar da cinikayya tsakaninsu.

  • Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida
  • Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano

Don haka kasashen biyu suka kirkiro da wani tsari kan yarjejeniyar musayar kudadensu, abin da zai baiwa Nijeriya damar yin amfani da Yuan, wato Renminbi kai tsaye wajen sayen kayayyaki daga China ba tare da yin amfani da dalar Amerika ba. An ko kirkiro da wannan tsari ne tun watan Afrilun shekarar 2018, wanda aka sabunta a watan Afrilun shekarar 2021, sannan kuma aka sake sabunta shi a karshen watan Disamban shekarar 2024.

Kudin Sin Yuan ya kasance daya daga cikin kudaden da hukumar bayar da lamuni ta kasa da kasa IMF ta amince da su. Wannan karbuwa da Yuan ta samu ya kara daga darajarta tare da samun karbuwa tsakanin kasashen duniya.

Aiwatar da wannan tsari yadda ya kamata, zai bunkasa cinikayya tsakanin Nijeriya da kasar Sin, tattalin arzikin Nijeriya zai samu tagomashi tare da samun karuwar aikin yi ga miliyoyin ’yan Nijeriya. Kana zai habaka zuba jari a fannoni daban daban tsakanin kasashen biyu, tare da rage dogaro da dalar Amerika. Wannan zai baiwa China da Nijeriya damar yaukaka dangantaka ta fannin kudade ta yadda hada hadar cinikayya za ta kasance babu tarnaki. ( Lawal Mamuda)

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

PDP Ta Soke Babban Taronta, Ta Dawo Da Anyanwu A Matsayin Sakatarenta

Next Post

Nazarin CGTN: Neman Kashe Kaso 5 Na GDP Kan Tsaro Ya Nuna Rashin Dabara Na NATO

Related

Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi
Ra'ayi Riga

Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

3 weeks ago
Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
Ra'ayinmu

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

4 weeks ago
Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba
Ra'ayinmu

Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

1 month ago
Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara
Ra'ayinmu

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

1 month ago
Daurarru
Ra'ayinmu

Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan

3 months ago
NCC
Ra'ayinmu

Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data

4 months ago
Next Post
Nazarin CGTN: Neman Kashe Kaso 5 Na GDP Kan Tsaro Ya Nuna Rashin Dabara Na NATO

Nazarin CGTN: Neman Kashe Kaso 5 Na GDP Kan Tsaro Ya Nuna Rashin Dabara Na NATO

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3

Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3

July 16, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

July 16, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno

July 16, 2025
Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?

EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari

July 16, 2025
Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

July 15, 2025
Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

July 15, 2025
VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

July 15, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

July 15, 2025
An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

July 15, 2025
Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

July 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.