• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunkurin Magance Dalar Shara A Kano

by Muhammad Awwal Umar
2 years ago
Kano

Tsawon lokaci a jihar Kano, duk inda ka duba sako da lungu musamman cikin birni, ban da tsibiri tsibiri na taragon shara, ba ka yin tozali da komai. An ta gabatar da tarin dalilai mabanbanta da ake tsammanin sune suka jaza wanzuwar wannan annakiya ta shara cikin birnin na Kano, duk da hadarin da take da shi ga fannin lafiyar jama’ar jihar. Ko babu komai, cutar maleriya ta sauro da kuma yiwuwa 6arkewar cutar kwalara, duka suna da alaka ta kusa da barin shara barkatai a muhallan jama’a ba tare da kawar da ita ba.

Illar barin shara barkatai a tsakanin al’uma, sha’anin ya kere batun 6arkewar cutuka ne kawai, lamarin kan yi sanadiyyar kawo ambaliyar ruwa, yayinda magudanan ruwan suka cushe, ba tare da an kawar da sharar da ta shake su ba. Duba da irin wadannan dalilai, duk wani shugaba, zai kwana ne da sanin wajibcin kawar da duk wata sharar da barin ta zai iya cutar da jama’ar da ke karkashinsa ta fuskoki da dama. Saboda barazanar da cakudin shara ke wa jama’ar ta Kano, shi ne babban dalilin da ya fizge mu zuwa ga jin ta-bakin babban daraktan hukumar kula da debe shara ta Kano a yau, wato Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago, wanda a fagen siyasar Kano aka fi saninsa da Danzago.

  • Malamai Sun Gargadi Tinubu Kan Daukar Matakin Soji A Kan Nijar
  • Mai Magana Da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Yi Karin Haske Kan Bayanan Kafofin Watsa Labarai Game Da Sanarwar Italiya Na Kin Tsawaita Yarjejeniyar Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Ambassador Danzago, ya yi wata shimfida ne yayin tattaunawar tamu, inda ya faro tun daga Shekarar 1999, lokacin da Engr Rabi’u Musa Kwankwaso ne gwamnan Kano. Har Kwankwason ya bar kujerar mulkin ta Kano, wannan ma’aikata ta shara na amsa sunan REMASAB (Kano State Refuse Management & Sanitation Board) ne. Haka, shi ma Malam Shekarau, tun da yake bisa kujerar gwamnan Kano, daga Shekarar 2003 zuwa 2011, bai canja sunan hukumar ba. Bugu da kari, da Kwankwaso da Shekarau, duka sun yi kokarin samar da kayan aiki ga wannan hukuma ta shara. Sannan, sa’adda maigirma Engr. Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo zangon mulkinsa na biyu a Shekarar 2015,  ya sake gwangwaje wannan hukuma ta Remasab da kayan aiki, irin wadanda ake matukar kishirwarsu a lokacin. Sabbin mabanbantan motoci kar na aikin shara kimanin guda arba’in da biyar (45) ne ya danka su ga hukumar ta Remasab. Sannan, har ya sauka, hukumar na karkashin kulawar gwamnati ne, damfare da sunanta da ta yi shuhura da shi, wato Remasab.

Ambassador Danzago ya kara da cewa,  tsohon gwamna Ganduje kuwa, wanda ya dare bisa kujerar gwamnan Kano a Shekarar 2019 zuwa 2023, ya sami hukumar ta Remasab karkashin kulawar gwamnatin Kano ne, amma gabanin saukarsa, sai ya gabatar da wata yarjejeniya tsakanin gwamnati da wani kamfani, ta yadda hukumar za ta tashi karkashin kulawar gwamnati zuwa ga wasu tsirarin mutane. Sai dai, tun kafin a je da nisa, sai wannan yarjejeniya ta ruguje, ko dai saboda wata kuskunda da aka samu ne daga wancan kamfani, ko kuma, watakil gwamnati ba ta tsaya tsai ta nazarci lamarin ba irin yadda ya kamata.

Ko da maigirma gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sami damar zama za6a66en gwamnan wannan jiha tamu ta Kano, sai ya nuna fa da gaske yake wajen yin duk mai yiwuwa wajen kawar da kazantar sharar da ta yi wa jihar Kano katutu ba tare da yin wata kasa a gwiwa ba, in ji Danzago. Sannan, tsohon sunan da aka san ma’aikatar da shi tun azal, wato Remasab, nan take sabon gwamna ya lashi takobin dawo mata da shi, tare da yin iya iyawarsa wajen dawo da wannan ma’aikata cikin haiyacinta.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

A kan hanyar cika kudirin gwamna na farfado da ran wannan ma’aikata in ji Danzago, shi ma shugaban hukumar sauraren korafe korafen jama’a ta Kano, Muhuyi Magaji R/Gado, ya shiga ya fita, har sai da ya dawowa da wannan hukuma wasu manyan motoci nata guda bakwai (7) da ma wasu, wadanda a baya aka sai da su ba bisa ka’ida ba. Yanzu haka, mun sa motocin na gudanar da aiyukansu a hukumar. Da yawan kayan wannan hukuma da aka sayar, Muhuyin, ya yi azamar dawo mana da su alhamdulillaHi.

Idan ba a manta ba, cikin wata jarida ta yanar gizo da ake kiranta da Dailynigerian.com, an jiyo mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D/Tofa na gabatar da wani zargi da ake yi wa tsohuwar gwamnatin Ganduje, na sayar da akasarin manyan kadarorin wannan hukuma ta Remasab,  cikin fakewa da kulla ciniki na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da wani kamfani, an sayar da su ne ga iyalai da kuma abokai, inda maigirma gwamnan Kano Abba Kabir ke fassara lamarin da wani abin kaico!.

Haka zalika, za mu yi duk mai yiwuwa, wajen ganin cewa iya wuraren da hukuma ta sahale ne kawai za a zuba shara a wurin. Ko alama, ba za mu lamunci jirkitar da shara barkatai a ko’ina cikin birni da kewaye ba, in ji Danzago.

Danzagon ya ci gaba da cewa,  mu na aiki ne yanzu haka dare da rana ba tare da kakkautawa ba. Dole ne shugaba ya fita, ba ya makale cikin ofis ba, ba tare da sanin abinda ke faruwa a waje ba. Shi shugaba, shi ne mai yi wa mutane hidima a ko da yaushe. Shi yasa lokacin da muka shiga aiki can “Yan dabino Yakasai lokacin da ake lafta mamakon ruwa, sai jama’ar unguwar suka rika mamakinmu. Ba wannan ma’aikata tawa ta Remasab ba kawai, kusan kowace ma’aikata na bisa sirdin aiwatar da aiyuka ne, duba da kalaman gwamna cewa, zuwa Watanni shida, duk wani da aka nada bisa wata kujera sai bai yi abin kirki ba, a fili ne yake cewa wannan mutumi ya sallami kansa da kansa.

Ambassador Danzago ya kara da cewa, yanzu haka suna nan suna tantance hakikanin ma’aikatansu a takarda, kuma za su bi su har wuraren da suke aiki don tabbatarwa. Bugu da kari, duk wani ma’aikacinmu da ke da wani hakki na gaskiya, a shirye muke da mu ba shi hakkin nasa.

Babu shakka, muddin kowace ma’aikata za ta tashi haikan wajen sauke nauyin da maigirma gwamna Abba Kabir Yusuf ya aza mata, la-budda za a haife da-mai-ido a Kano.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Manchester United Za Ta Bayyana Matsayarta A Kan Greenwood

Manchester United Za Ta Bayyana Matsayarta A Kan Greenwood

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.