Daya daga cikin abinda ke ciwa fannin aikin noma Tuwo a Kwarya a nahiyar Afirka shine karancin takin zamani.
Sai dai, domin a lalubo da mafita kan wannan kalubalen, wasu hukumomi sun dukufa kan yadda za su manoma a nahiyar sun samar wa da manoma takin, musamman kan farashi mai sauki.
- An Jefar Da Jariri Dan Kwana 2 A Sansanin ‘Yan Gundun Hijira A Edo
- Sudan: Jami’o’in Nijeriya Sun Sha Alwashin Bai Wa Daliban Da Aka Kwaso Guraben Karatu
Misali, hukumar samar da abinci da kuma bunkasa aikin noma da ke a karkashin majalisar dinkin duniya FAO da kuma shirin samar da abinci da ke a karkashin majalisar WFP sun yi hasashen cewa, za a samu karancin abinci saboda tarnakin da fannin na samar da abinci ke fuskanta.
Bugu da kari, don a magance irin wannan kalubalen, masu ruwa da tsaki a fadin duniya a fannin aikin noma sun gudanar da taro, inda suka yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a yi amfani da kayan aikin noma na zamani, musamman don a tabbatar kananan manoma sun samu takin zamani kuma kan lokaci don a samar da abinci, musamman mai gina jiki ga alumma.
Wasu daga cikin tattaunawar da aka yi irin wannan tarukan, sun nuna yadda wasu yankunan da ke a nahiyar Afirka ke kan yin kokari wajen samar da wadatacen takin zamani da ilimantar da manoman kan sanin ingantacciyar kasar noma da za su yi shuka akai da yadda za su zuba takin zamani da sauransu.
Har ila yau masu bayar da dauki a fannin aikin noma sun zuba dala biliyan 30,musamman don a bunkasa yin noma a nahiyar Afirka ke na sama da shekaru hudu masu zuwa.
Baya ga wannan, mahalarta taron sun kuma yi kira da a gaggauta samar da takin zamani ga manoman da ke a nahiyar kuma a cikin farashi mai sauki.
A cewar kungiyar masana’antun sarrafa takin zamani ta kasa da kasa, a nahiyar Afirka IFA, ana yin amfani da buhun takin zamani mai nauyin kilo 12 a kowacce kadadar noma daya.
Hakazalika, Cibiyar bincike kan tsare -tsaren abinci ta kasa da kasa IFPRI ta bayyana cewa, takin zamani da moma ke yin amfani da shi a Nijeriya da Kenya da kuma wasu sassan a Afrika ako wacca kadadar yin noma, ya kai kasa da kilo 50 idan aka yi la’akari da yadda ake yin amfani da shi Malaysiya, inda ake yin amfani da akalla kilo 1,570 ako wacce kadadar noma daya sai kuma a kasar Hong Kong, inda ake yin amfani da kilo 1,297 ako wacce kadadar noma daya, inda kuma a kasar Bangladesh ake yin amfani da akalla kilo 278 ako wacce kadadar noma daya.
Bugu da kari, Cibiyoyi ta IFPRI ita ma ta goyi bayan taron musamman don tattauna wa kan yadda za a samar wa da manoma da ke a nahiyar takin zamani da kuma samar wa masu safarar takin kudade don a shigo da sanadaran da ake sarrafa takin zamanin.
Hakazalika, kulab din da ke samar wa da manoma takin zamani wato Afrikom, shi ma ya gudanar da wata ganawa a Accra, babban birinin kasar Ghana kan yadda za a samar wa da manoma takin zamani.
Kulab din ya gudanar da ganawar ce wadda ta kasance a karon farko bisa hadaka da Cibiyar habaka takin zamani ta kasa da kasa IFDC tare da kuma kungiyar samar da takin zamani a yammacin Afrika WAFA.
Sun yi hakan ne bisa kokarin yadda za a samar wa da manoma takin zamani a Afrika da kuma irin sauye -sauyen da aka samu a fannin na samar da takin zamani a Afrika.