ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisa A Turkiyya

by Muhammad
3 years ago
Turkiyya

A yau masu zabe daga fadin Turkiyya za su nufi rumfunan zabe domin kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

An fara zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a fadin Turkiyya da safiyar Lahadi. Shugaban kasa mai ci Recep Tayyip Erdogan yana neman wani wa’adi sa’annan daga bangaren adawa Kemal Kilicdaroglu na Nation’s Alliance da kuma Sinan Ogan na Ata Alliance su ma suna takarar.

  • Yunkurin Masu Ruwa Da Tsaki A Nahiyar Afirka Wajen Samar Da Takin Zamani

Kafar yada labaran kasar TRT HAUS ta ce, Hukumar zaben Turkiyya mai zaman kanta YSK ta sanar da cewa sama da ‘yan kasar miliyan 64 ne suka cancanta su jefa kuri’a a zaben 14 ga watan Mayu, daga cikin har da masu zabe sama da miliyan uku da ke a kasar waje.

ADVERTISEMENT

Za a kammala jefa kuri’a da misalin karfe 5:00 agogon Turkiyya, haka kuma ana sa ran sakamako farko zai soma shigowa ba da jimawa ba.

Ana bukatar masu zabe a Turkiyya su nuna katin shaidarsu na dan kasa da sauran katukan da ake bukata a rumfar zabe domin jefa kuri’a.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

Daga nan ne ake ba mai zabe takardun jefa kuri’a biyu, daya ta shugaban kasa sai kuma daya ta ‘yan majalisa. Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa ba a yarda masu zaben su dauki hoto ko bidiyo ba a wuraren zaben, kuma ana bukatar su bar wayoyinsu a waje.

Bayan an kammala zaben, kuri’un da aka jefa na shugaban kasa ana kirga su a gaban kwamitin zaben wanda ya kunshi jami’an hukumar zaben da kuma wakilan jam’iyyu da kuma jama’ar da suka yi zaben.

Duka ‘yan kasa za su iya zabe Hukumar zaben Turkiyya ta dauki matakai domin tabbatar da cewa ta sa zaben ya zo da sauki ga duka jama’ar kasar ko da suna da bukata ta musamman.

Ga wadanda ba za su iya barin gidajensu ko kuma gadon asibitinsu ba, akwai akwatunan zabe na tafi da gidanka da aka tanadar.

Za a kai wadannan akwatuna inda suke domin ganin cewa sun yi zabensu. Wata mafita kuma ita ce za a iya amfani da motar kwana-kwana ta asibiti domin kai marar lafiya jefa kuri’a a kyauta.

Haka kuma hukumar zaben ta tanadi takardun zabe na musamman ga masu larurar gani. Wadannan takardun suna da gwaragwaran rubutu da kuma haruffan makafi domin su iya zabe ba tare da an tallafa musu ba.

Duka wadannan tsare-tsaren an yi su ne domin tabbatar da cewa duka jama’ar kasar za su iya zabe cikin martaba. An kawo kuri’un ‘yan Turkiyya mazauna kasar waje ta jirgin sama kuma za a kirga su a lokacin daya da wadanda aka jefa a Turkiyya.

An soma jefa kuri’u a kasashen waje tsakanin 27 ga watan Afrilu aka kammala 9 ga watan Mayu.

A babban zaben, dole ne jam’iyya ta samu akalla kashi 10 na kuri’un da aka jefa a fadin kasar kafin dan takararta ya samu kujera a majalisa.

Jam’iyyun hadaka ne kawai za su wuce kashi goma ga jam’iyyunsu su samu kujera. A ranar zabe, an haramta wa duk wata kafar watsa labarai saka duk wata talla ta siyasa ko hasashe ko kuma sharhi kan siyasa har zuwa karfe 6:00 na yamma (1500GMT).

Tsakanin 06:00PM (1500GMT) da 9:00PM (1800GMT), kafafen watsa labarai za su iya wallafa sanarwa kan zabe wadda hukumar zabe ta bayar.

Haka kuma za a haramta sayar da barasa daga 6:00 na safe (0300GMT) zuwa 12:00 na dare (2100GMT), haka an haramta shan giya a bainar jama’a.

Turkiyya
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano

MASU ALAKA

Turkiyya
Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Turkiyya
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Turkiyya
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Dakatar Da Shigo Da Manja: Kwararru A Nijeriya Sun Bukaci A Zuba Jari Mai Yawa A Fannin

Dakatar Da Shigo Da Manja: Kwararru A Nijeriya Sun Bukaci A Zuba Jari Mai Yawa A Fannin

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Turkiyya

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Turkiyya

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.