• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson

by Naziru Adam Ibrahim
4 months ago
2027

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu, ya fi mayar da hankali kan harkokin siyasa da shirye-shiryen zabɓen 2027 fiye da gudanar da mulki, inda ya ke watsi da aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar nan don ci gaban ƙasa.

Dickson ya bayyana hakan ne yayin muhawarar kan wani ƙudiri da Sanata Solomon Adeola, mai wakiltar Ogun ta Yamma, Shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, ya gabatar don tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin shekarar 2024 zuwa ƙarshen Disambar 2025.

  • Hatsarin Kwale-kwale: Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya Ta Ceto Jami’an ‘Yansanda 8 Da Wani A Bayelsa
  • Kotu Ta Daure Uban Da Ya Dirka Wa ‘Yarsa Ciki A Bayelsa

A cewarsa, har yanzu ‘yan Nijeriya ba su amfana da ɓangaren ci gaba na kasafin 2024 da Majalisar ta amince da shi ba, duk da cewa an riga an fitar da kuɗaɗen da suka shafi gudanarwa da albashi wanda ke cikin kasafin na yau da kullum, amma ba a aiwatar da na ɓangaren ayyukan ci gaba da jin dadin jama’a ba.

Sanatan ya bayar da misali da rahotannin da ke nuna cewa wasu ‘yan kwangila da suka kammala ayyukan gwamnati na ci gaba suna zanga-zanga saboda rashin biyan su hakkokinsu.

Ya kuma nuna damuwa cewa gwamnatin na kau da kai daga nauyin da ke kanta saboda siyasa, musamman shirye-shiryen zaɓen 2027 da kuma yawaitar masu sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya yi gargaɗi cewa ɓangarorin zartarwa da na dokoki na barin nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

Dickson ya goyi bayan buƙatar gudanar da bincike kan jinkirin aiwatar da kasafin yana mai jaddada cewa matsalar ba ta shafi rashin kudi ba tare da kira ga majalisar ta umarci kwamitocin kasafin kudi su gudanar da bincike cikin mako guda su kuma kawo rahoto.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
Siyasa

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump
Labarai

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

LABARAI MASU NASABA

Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.